Delta: ‘Dole waɗanda suka kashe sosjoji su fuskanci hukunci’ — Tinubu

Daga BASHIR ISAH

Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya yi tir da kashe sojoji da aka yi a Jihar Delta, yana mai cewa dole waɗanda suka aikata wannan ɗanyen aikin su fuskanci hukunci.

Kwanan nan ne aka kashe wasu sojoji 15 a jihar ta Delta, ciki har da manjo guda biyu, kyaftin ɗaya, sai kuma ƙananan sojoji 12 da farar hula ɗaya.

Lamarin ya faru ne a yankunan Okuama da Ughelli a makon da ya gabata a lokacin da suka tafi aikin kwantar da tarzoma.

Sai dai, da yake maida martani kan lamarin a cikin sanarwar da ya fitar da yammacin Lahadi, Shugaba Tinubu ya bayyana kisan a matsayin mummunan al’amari.

Tinubu ya yi amfani da wannan dama wajen nuna alhini da kuma jajanta wa gwamnati da ‘yan uwan sojojin da lamarin ya shafa.

Haka nan, ya jinjina wa marigayan bisa jajircewarsu da kuma yadda suka amsa kiran mahalicci yayin da suke tsaka da yi wa ƙasa hidima.