An tsinci jariri a Nasarawa

Daga JOHN D. WADA, a Lafiya

Wani matashi mai suna Yakubu Sule ya sinci wani jariri mai watanni biyu kacal da haihuwa wanda har yanzu ba a san wace ta jefar da shi a wata unguwa da ake kira Unguwar Maina dake birnin Lafiya, Jihar Nasarawa ba.

Binciken wakilin mu ya gano cewa an tsinci jaririn ne shinfiɗe a ƙasa a ƙofar wani gida dake kusa da ofishin hukumar kula da gidan yari a da ke Unguwar Maina ɗin.

Da yake bayyana wa wakilin mu yadda lamarin ya auku, wanda ya tsinci jaririn, wato Yakubu Sule ya ce, ya ga jaririn ne shimfiɗe a ƙasa da mitsalin ƙarfe 11 da rabi na dare.

Acewarsa, dafarko ya ga wani abu ne mai kama da alamar mutum inda nan take sai ya sake matsawa kusa inda a nan ya gano cewa jariri ne.

Ya ƙara da cewa, daga nan ne sai ya dudduba ko zai ga mahaifiyar jaririn amma bai ga kowa ba.

Ya ce sai ya ɗauki jaririn ya kai shi gidansa, wanda a cewarsa da farko hakan ya so ya haifar da matsala tsakaninsa da mai ɗakinsa don ya tashe ta daga barci gane da jaririn.

Ya ci gaba da cewa, “Matata da sauran makotanmu baki ɗaya ba su iya barci ba a daren saboda kukan da jaririn ya riƙa yi.

“A ƙarshe sai da na ɗauke shi na riƙa wasa da shi kafin daga bisani barci ya ɗauke shi.” Inji Yakubu Sule.

A anasa ɓangaren, mai unguwar Maina, Malam Idris Muhammad, ya tabbatar wa wakilin namu cewa bayan an sanar da shi aukuwar lamarin sai ya sanar da ‘yan sanda don a ɗaukar matakin da ya dace.

Ƙoƙarin da wakilinmu ya yi don jin ta bakin mai magana da yawun ‘yan sandan jihar, ya ci tura.