Ina mafita ga Almajiranci?

Assalamu alaikum.

A yau zan aika buɗaɗɗiyar wasiƙa ne na ina mafita ga Almajiranci a Nijeriya.

Almajiranci na da ma’ana guda biyu, wato tsarin koyar da ilimin addinin musulunci a ƙasashen yammacin Afirka, musamman a arewacin Nijeriya, yadda ake tura yara wajen Malamai a wasu garuruwa domin yin karatun Ƙur’ani. Ɗaya ma’anar ita ce ta tsarin da irin waɗannan ɗalibai da kuma waɗanda ba ɗaliban ba ke yawo su na barar abinci ko kuɗi.

Almajirancin da mu ke gani a yanzu ya sha banban da wanda aka gada a can baya. A baya almajiranci shine rumbun da ake samar da Malamai, limamai da masu wa’azi, domin a doron wannan tsari ne Usman Ɗanfodio ya taso har ya yi jihadin da ya samar da daular Usmaniyya wadda ta ture mulkin zalunci na habe ta kafa daular musulunci mai adalci, zaman lafiya da ilimi a yawancin sassa na arewacin afirka kusan sama da shekaru ɗari.

Wayewar rubutu da karatu na ajami ya samar wa daular damar kafa tsari na mulki a faɗin daular cikin sauƙi. Makarantun allo su ne su ka zama wasu jami’o’i da ke samar da ƙwararrun Malamai da ɗalibai cikin tsarin tarbiyya, juriya da girmama na gaba. Zuwan turawa sun kwaikwaiyi tsarin ta hanyar samar da makarantun kwana na boko.

Bayan turawa sun kafa mulkinsu na mallaka, cikin kutungwila, sun kawo canje-canje waɗanda su ne ummul aba’isun karya tsarin makarantun allo. Ragewa sarakunan gargajiya iko, waɗanda su ke bawa Malaman allo gonaki waɗanda almajiransu ke nomawa domin samar da abincin da za su ci, sannan su ke tattara sadaka da zakka da ake kaiwa makarantun, ya kawo durƙushewar tsarin ciyarwa a makarantun allo.

Iyaye na kawo amfanin gonar da suka shuka wajen Malaman domin ciyar da yaransu da ke almajiranci. Rushewar wannan tsari ya jawo dole Malamai ke tura yaransu yin bara domin samo abincin da za su ci. Sannan a baya ana tura yara almajiranci bayan sun tasa sosai sun kai shekaru goma zuwa sama. Haƙiƙa zuwan bature na daga cikin abinda ya fara karya tsarin almajiranci.

A yau almajiranci ya rasa irin darajojin da aka san shi da su a baya ya zama wata annoba ga almajiran kansu, malamansu, iyayensu da kuma al’umma. Domin a yanzu ka na iya ganin yaro ɗan shekara 4 an turo shi almajiranci, abinda babu shi a baya. Rashin imani ne idan aka kalla ta kowacce fuska, walau ta fuskar addini, al’ada ko tattalin arziki, tura ɗan ƙaramin yaro mai shekara huɗu zuwa almajiranci ko da Almajirci irin na da ne ba na yanzu ba. A addinance ko sakin matarka ka yi ba ka da ikon karɓe yaro da ya gaza shekaru 7 aƙalla. Sannan binciken kimiyya ya tabbatar da cewa shi yaro daga haihuwa zuwa aƙalla shekaru 10 ya na buƙatar kasancewa kusa da uwarsa domin Allah ya halicci mutum da ɗabi’u waɗanda sannu a hankali su ke bayyana daki-daki a rayuwar yara sakamakon mu’amala da uwa, uba, ’yanuwa da makwabta. Misali halayyar tausayi ko soyayya ko sanin ya kamata mu’amala da uwa ke saka na yaro su bayyana gare shi kum ya gane ya riqe su a kwakwalwarsa.

To a duk sanda aka raba yaro da uwarsa ya na rasa wannan mataki da ke zungurar boyayyun halayensa. Binciken shahararren masani Sigmund Freud ya tabbatar da cewa akasarin mutane da ke zama mugaye marasa imani a lokacin da su ka girma, idan an binciki shekarun yarintarsu akan tarar sun rasa waccan irin kyaykyawar mu’amala musamman da uwa.

Sakamakon haka su kan kasance marasa tausayi kuma ɗabi’ar da ke saka da-na-sani na da rauni cikin halayyarsu. Abubuwan da ke faruwa yau a arewacin Nijeriya na tabbatar da gaskiyar wannan bincike saboda yawancin ‘yan boko haram da masu satar mutane na da irin wannan halayya ta rashin imani da halin da-na-sani. Domin sun taso babu shakuwar iyaye da al’umma don haka su ke kallon kowa a matsayin makiyi saboda su ma babu wanda ya tausaya musu.

Asarar da tsarin almajiranci ke jawo mana na da yawa: ya na hana yara ilimi, samun soyayyar iyaye, jefa su cikin haɗurra da ke tauye rayuwarsa ko zama annoba ga al’umma. Dole duk masu ruwa da tsaki, musamman hukumomi su haɗa ƙarfi da ƙarfe wajen ganin an kawo canji a tsarin, ta hanyar saka shi cikin tsarin ilimi na ƙasa.

Wassalam.

Mustapha Musa Muhammad, 08168716583.