Jerin sunayen sojoji 15 da suka cimma ajali a Delta

Daga BASHIR ISAH

Rundunar Sojin Nijeriya ta fiitar da jerin sunayen dakarunta da suka rasa rayukansu a bakin aiki a Jihar Delta kwanan nan.

Sojojin da lamarin ya shafa suna aiki ne a bataliya ta 181 Amphibious Battalion, sun mutu ne yayin da suke aikin wanzar da zaman lafiya domin kwantar da tarzoma a ƙaramar hukumar Bomadi ta jihar Delta sakamakon ɓarkewar rikici.

Rundunar ta ce sojojinta 15 tsagerun Niget Delta suka yi wa kisan gilla.

Jami’an da lamarin ya shafa sun haɗa da:

– LT COL AH ALI COMMAND OFFICER 181 AMPHIBIOUS BATTALION NIGERIAN ARMY

– Maj SD Shafa (N/13976)

– Maj DE Obi (N/14395)

– Capt U Zakari (N/16348)

– SSgt Yahaya Saidu (NA/36/2974)

– Cpl Yahaya Danbaba (1ONA/65/7274)

– Col Kabiru Bashir (11NA/66/9853)

– LCol Bulus Haruna (16NA/TS/5844)

– Lal Sole Opeyemi (17NA/760719)

– LCpl Bello Anas (17NA/76/290)

– LCpl Hamman Peter (NA/T82653)

– LCpl Ibrahim Abdullahi (18NA/77/1191)

– Pte Alhaji Isah (17NA/76/6079)

– Pte Clement Francis (19NA/78/0911)

– Pte Abubakar Ali (19NA/78/2162)

– Pte Ibrahim Adamu (19NA/78/6079)

– Pte Adamu Ibrahim (21NA/80/4795)