Sojoji sun ceto mutum 16 da aka yi garkuwa da su a Kajuru

Daga BASHIR ISAH

Rundunar Sojin Nijeriya ta bayyana cewa, dakarun da aka tura Jihar Kaduna ƙarƙashin shiyyar 1 Division, sun samu nasarar ceto mutum 16 da aka yi garkuwa da su a ƙauyen Tantatu cikin yankin Ƙaramar Kajuru a jihar.

Ta bayyana hakan ne cikin sanarwar da ta fitar a ranar Talata.

Rundunar ta ƙara da cewa, bayan da maharan suka yi garkuwa da wasu mutanen ƙauyen Tantatu a ranar 17 ga Maris, 2024, daga baya dakarun suka bi sawun ɓarayin.

“Bayan da suka isa wurin da lamarin ya faru, cikin ƙwarewa dakarun suka bi sawun maharan tare kuma da yin musayar wuta a tsakanin ɓangarorin biyu wanda aka ƙarshe dakarun suka samu nasarar kuɓutar da mutum 16 da aka yi garkuwa da su,” in ji sanarwar.

A cewar sanarwar mai ɗauke da sa hannun Manjo Janar Onyema Nwachukwu, dakarun na ci gaba da bincike a dajin da maharan suka ɓuya don ci gaba da kuɓutar da waɗanda ke hannun ‘yan bindigar.

Babban Hafsan Sojin Ƙasa, Lt Gen Taoreed Abiodun Lagbaja, ya yaba wa dakarun bisa wannan gagarumar nasarar da suka samu.

Kana ya buƙace su da su ƙara himma domin ganin bayan ‘yan ta’addan a ƙasar.