Illar cin hanci da cin dunduniya

Assalamu alaikum!

Yawancinmu ’yan Nijeriya mu kan kasance Jahilan masu ilimi ne, wato za ka ga cewa duk da cewa mun yi mu’amala iri-iri ta rayuwa kuma mun je makaranta mun sami difloma, digiri ko digirgir, tunanin mu yakan kasance a gajeriyar mahanga yadda komai mu ke kallonsa daga ɓangaren yanki, addini ko ƙabila, kamar yadda malamai ke yawan cewa, shi jahilci ba wai kawai yana nufin rashin iya karatu ko rubutu ba ne, fyace ana aiki da shi yadda ya kamata.

Mu yi ƙoƙarin ganin ba mu zama misalin Jaki da kaya ba. Mun kasa gane cewa manyan ƙasarnan sun kasance a mu’amalar rayuwarsu da ta ’ya’yansu babu ruwansu da addini, qabila ko yanki, su kan haɗa kai wajen ganin sun sace arzikin ƙasa da barin talakawa cikin wahala. Duk matsalolin da ‘yan Nijeriya ke fuskanta a yanzu idan ka bi asalai za ka iya alaƙanta sanadiyar daga cin hanci da rashawa.

’Yan Nijeriya mu farka daga barci, mu tashi tsaye wajen yi wa kan mu adalci. Mu riƙa kallon ƙasarmu ta mahangar gaskiya, ‘yan uwantaka da tsira tare ba ta mahangar vangaranci kowanne iri ba.

Mun fi kowa son addini, musulminmu da kiristanmu, ga yawan faɗar Allah a baki ko yaushe, amma babu Allah cikin zukatanmu. Annabi isa na cewa, “Gaskiya ce kaɗai za ta tserar da mu”, sannan mu ɗin ga yi wa mutane hukunci kawai daga irin aikin da su ka aikata.

A Ƙur’ani Allah ya umarce mu da mu zama masu adalci da faɗar gaskiya ko a karan kanmu ko iyaye da ‘yanuwa ba banbanci tsakanin attajiri da mawadaci. Mu haɗa hannu mu yaƙi cin hanci da rashawa mu kashe ta da kanmu.

Daga Ahmad Musa, 07066778190.