Hukumar tace finafinai ta bada umurnin rufe dukkan gidajen gala da ke Kano

Daga AISHA ASAS

Hukumar tace finafinai ta Jihar Kano, ƙarƙashin jagorancin Abba El-Mustapha ta bayar da umurnin kulle duk wani gidan gala da ke faɗin Jihar Kano. Wannan na daga cikin shirye-shiryen da hukumar ke yi na tarbon wata mai tsarki, watan Ramadana.

Sanarwar wadda ta fito ta hannun jami’in hulɗa da jama’a na hukumar, Abdullahi Sani Sulaiman.

A cewar sanarwar, hukuncin na zuwa ne bayan wata ganawa da shugaban hukumar ya yi da jagororin koungiyar ta masu gidajen gala a ofishinsa.

Kamar yadda ya bayyana, shugaban hukumar Abba El-Mustapha, ya ce, dokar za ta fara aiki ne a ranar Lahadin da ta gabata, kuma ba za ta tsaya ba har sai ranar 1 ga watan Shawwal, wanda zai yi daidai da ranar bikin karamar sallah.

Baya ga haka, hukumar ta gargaɗi masu gidajen wasan na gala da su goji karya wannan doka, domin hukunci mai tsauri zai sauka ga wanda aka kama da laifin bijirewa wannan doka, wanda zai iya kai ga rasa lasisin sa na din-din-din.

Hakazalika shugaban Abba El-Mustapha ya godewa jagororin ƙungiyar da ma ‘yan ƙungiyar bakiɗaya tare da al’ummar Jihar Kano, kan goyon bayan da suke ba wa hukumar a kodayaushe.

Daga ƙarahe ya ƙara tunatar da al’umma cewa, ƙofarsa a buɗe take a kodayaushe don karɓar shawarwari, ko sanar da hukumar wani abu da zai taimake ta wurin ganin ta kai ga nasara kan ayyukan da ta sa gaba.