Yadda jarumi Ali Nuhu ya karɓi ragamar aiki a matsayin Shugaban NFC

Daga AISHA ASAS

A ranar Talata da ta gabata ne, shahararren jarumi a masana’antar Kannywood Dakta Ali Nuhu ya kama aiki a hukumance a matsayin Shugaban Hukumar Finafinai ta Qasa (NFC) tare da alƙawarin hanzarta kawo cigaba a masana’antar finafinan Nijeriya.

Bayanin wanda ya fito daga wurin Daraktan Ya daa Labarai na hukumar, Mista Brian Etuk.

A sanarwar wadda ya gabatar ga ‘yan jarida, Mista Brian ya ce, a ƙwarya-ƙwaryar bikin miqa mulki da aka gudanar a shelkwatar hukumar da ke Jos ta Jihar Filatu, wanda ya samu halartar manyan baqi, da suka haɗa da jiga-jigan masana’antar fim, ma’aikatan hukumar da kuma manyan ma’aikatan gwmamnati, Ali Nuhu ya ce, ya ɗora aniyyar yin amfani da ilimin sanin makamar aiki da yake da shi wurin tsara yadda zai gudanar da aikin da zai ciyar da masana’antar finafinan Nijeriya gaba.

Jarumin wanda ya kasance na bakwai a jerin waɗanda suka riƙe hukumar ya bayyana irin tsammanin Gwamnatin Tarayya, finafinai, masu ruwa da tsaki tare da ɗaukacin al’ummar Nijeriya kan irin rawar da ake sa ran hukumar ta taka.

Ya kuma bayar da tabbacin zai jagoranci hukumar zuwa ga cigaban da ba a tava samu irinsa ba a tarihin hukumar.

Ali Nuhu ya zayyano tsare-tsare na ingantattun aiyyuka na masana’antar finafinai da zai gudanar, inda ya ce, za a haɓaka horaswa, inganta kayan aiki don havaka masana’antu, don samun ingantattun finafinai da za a kalla a cikin qasa da waje, sannan hukumar za ta yi haɗin gwiwa da manyan hukumomi da ƙungiyoyi na gwamnati da masu zaman kansu, don haɓaka harkar ƙirƙira tare da janyo hankali don zuba jari a harkar finafinai tare da sauƙaƙa haɗin gwiwa a harkar fim.

Baya ga haka, Ali ya nuna matuqar godiya da jin daɗinsa ga shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, kan muƙamin da ya ba shi, kamar yadda ya yaba tare da alƙawarin tallafa wa manufofin Minista Hannatu Musawa, wurin bunƙasa harkar finafinai.

A nasa jawabin Mista Edmund Peter, daraktan shirye-shirye da bada tallafi ga industiri, ya ce, hukumar ta samu nasarori masu yawa tun lokacin da aka kafa ta a shekarar 1979. Sannan ya bayyana ƙwarin gwiyar da masu gudanarwa da ma’aikatan hukumar suke da shi kan yadda Ali Nuhu zai jagoranci hukumar zuwa ga cigaba mai ɗorewa.

“Babbar nasara ce samun jajirtattun ma’aikata da suke shirye don ba ka goyon baya a lokacin da ka fara wannan sabuwar tafiya, ta hanyar amfani da ƙarfin hukumar don faɗaɗata zuwa ga babbar hukumar cigaban fannin finafinai,” inji Peter.

Daga cikin mahalarta taron akwai; Malam Abba El-Mustapha, Babban Sakataren Hukumar Tace Finafinai ta Jihar Kano, Alhaji Sani Muazu, tsohon shugaban Ƙungiyar Masu Finafınai ta Nijeriya (MOPPAN), Barista Ezra Jinang, babban mai tallafa wa gwamnan Filato kan Ƙirƙira da Nishaɗi, Alfred Mgbejume, Achor Yusuf, da Umar Tanko Ravi, Baballe Hayatu, Adam A. Zango, Al-Amin Buhari, Yusuf Lazio, Lawal Ahmad, wakilan shugabannin ƙungiyar ‘yan wasan kwaikwayo ta Nijeriya (AGN), ƙungiyar daraktoci ta Nijeriya (DGN) da Ƙungiyar Masu Shirya Finafinai ta Nijeriya (MOPPAN), Sir Eward Fom na ƙungiyar masu shirya finafınai (AMP), da kuma masu shirya finafinai da dama.

Da yake nasa jawabin taya murna, shugaban Ƙungiyar kwararru ta masu shirya finafinai, MOPPAN, Alhaji Habibu Barde, ya nuna matuƙar jin daɗinsa da samun muƙamin da jarumin masana’antar Kannywood Ali Nuhu ya yi, a wata sanarwa da ta fito, inda yake cewa, “Mun yi matuƙar murna da wannan cigaba da aka samu a harkar fim, da kuma samun ɗaya daga cikinmu a matsayin sabon Shugaban Hukumar Finafinai ta Ƙasa. Wanda ya karɓi aiki a jiya, a gaban masu ruwa da tsaki da kuma waƙilan Ƙungiyar MOPPAN.

Muna da tabbaci tare da ƙwarin gwiwa kan Dakta Ali Nuhu, game da shugabantar al’amura, NFC za ta samu cigaban da ba ta tava samu ba, domin zai yi amfani da ɗimbin qwarewa da ilimin da yake da shi da kuma hikima wurin ganin ya ciyar da hukumar gaba a matakin ƙasa da kuma duniya bakiɗaya.”

Daga ƙarshe Barde ya taya jarumin murna tare da tabbatar da goyon bayan ƙungiyar MOPPAN da kuma ba shi haɗin kai wurin ganin ya gudanar da aiki cikin sauƙi.