Lawal ya kama hanyar bunƙasa Asibitin Ƙwararru na Zamfara

*Ya jagoranci zaman Majalisar Zartarwa Karo na 19

Daga BASHIR ISAH

Gwamna Dauda Lawal na Jihar Zamfara ya amince da a yi wa Asibitin Ƙwararru na Yeriman Bakura kwaskwarima domin cimma buƙatun kiwo lafiya yadda ya kamata a jihar.

Lawal ya amince da wannan aikin ne yayin zaman Majalisar Zartarwar karo na 19 wanda ya jagoranta a ranar Litinin a Fadar Gwamnatin jihar da ke Gusau, babban birnin Jihar.

Sanarwa mai ɗauke da sa hannun Kakakin Gwamna, Sulaiman Bala Idris, ta ce aikin gyaran asibitin zai kan kama ba tare da ɓata lokaci ba, inda ake sa ran bunƙasa cibiyar daidaida da zamani kuma mai ɗauke da ingantattun kayayyakin aiki irin na zamani.

Sanarwar ta ce, “Asibitin ya kasance cikin hali mara kyau da daɗewa, sannan ga ƙarancin kayan aiki.

“Wannan ya sa dole akan ɗauki mara lafiya zuwa Sokoto ko Kaduna don kula da matsalar ƙoda da sauran rashin lafiya masu tsanani.”

“Daraktan Cibiyar Minjirya Health Services Limited, Alhaji Mustapha Falaki, shi ne ya gabatar da bayani kan halin da asibitin ƙwararrun ke ciki da kuma matakai na gaba da ake shirin ɗauka don yi wa asibitin gyaran fuska,” in ji sanarwar.

Sanarwar ta ƙara da cewa, an tattauna batutuwa da dama yayin zaman Majalisar, ciki har da batun kare walwalar al’ummar jihar da dai sauransu.