Daga JOHN D. WADA, a Lafiya
Gwamnan jihar Nasarawa, Injiniya Abdullahi Sule, ya shawarci ɗan takaran shugaban ƙasa a jam’iyyar Labour, Mista Peter Obi, kan ya riƙa bai wa Shugaba Bola Ahmed Tinibu cikakken goyon baya a ƙoƙarin da yake yi na kai ƙasar nan mataki nagaba.
Gwamnan ya bayyana haka ne a lokacin da Obi ya ziyarce shi a Gidan Gwamnati dake birnin Lafiya, babban birnin Jihar Nasarawa, a rabar Litinin, 18 ga Maris, 2024.
Gwamna Sule ya gode wa Peter Obi dangane da ziyarar ta musamman da ya kai masa, inda ya ce Obi yana da komai da ya dace wajen bai wa Shugaba Tinubu goyon baya da yake buƙata don samun nasarori wa ‘yan Nijeriya baki ɗaya.
Ya ce, “Ina so in sake gode maka sosai game da ziyarar da ka kawo min wanda ke nuni cewa akwai lokacin siyasa akwai kuma lokacin zumunci, sannan ina so in yi amfani da damar nan in yi kira a gare ka cewa ka taimaka ka riƙa tallafa wa gwamnatin Tinibu a koyaushe maimakon ci gaba da kasancewa ɗan hamayyar gwamnatin sa don ƙalubalen ƙasar nan mutum ɗaya ba zai iya magance su ba.”
Tun farko a jawabinsa Obi ya bayyana wa Gwamna Sule cewa, ya kasance a gidan gwamnatin ne don ya ziyarce shi na musamman, ya kuma sanar da shi cewa a yanzu haka yana bin duka jihohin ƙasar nan inda yake aiwatar da wasu ayyukan ci gaba da suka haɗa da gina rijiyoyin burtsatse da sauran su wanda jihar ta Nasarawa ma za ta amfana.
Daga nan, ya buƙaci gwamnan da ba shi haɗin don cimma nasarar ayyukansa a jihar.
