Na’ibin limamin masallacin gidan Sarkin Kano, Malam Nazifi ya rasu

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano

Allah ya yi wa na’ibin limamin masallacin Juma’a na gidan sarki, Malam Nazifi Muhammad Ɗalhatu, rasuwa a yammacin Talata.

Rahotanni sun bayyana cewar Marigayin ya rasu yana da shekaru 81, bayan fama da rashin lafiya.

An yi jana’izarsa a harabar masallacin gidan Sarkin Kano da ke Ƙofar Kwaru.

Rahotanni sun ce jama’a da dama ne suka halarci jana’izar ne, daga ciki har da Mai Martaba Sarkin Bichi, Alhaji Nasiru Ado Bayero da sauransu.