Matan aure barka da Ramadan! (2)

Tare da AMNINA YUSUF ALI

Assalamu alaikum, uwargida da kuma amarya. Ina yi muku sannu da ibada a wannan wata mai alfarma. Fatan Allah ya ba mu dacewa a cikinsa. Har yanzu dai muna kan maudu’in nan namu na sanar da girke-girke ga mata masu aure saboda shigowar watan Ramadan mai albarka domin su sauya wa Maigida samfurin tukunya domin samun ninkin ƙarin lada da watan Ramadan watan rahma da yafe zunubai da ɗaga darajar bayi tare da amsa dukkan buƙatu.

Allah ya yi mana katari da dukkan romo da falaloli da suke a wannan wata. Kuma Allah ya nuna mana ƙarshensa cikin ƙoshin lafiya. Sannan kuma muna kira da matan aure a yi girke-girke, amma a ware lokacin ibada. Domin yadda faranta ran mai gida yake da muhimmanci haka ma yin ibada mai yawa a watan nan take da muhimmanci da falala.

A makon da ya gabata mun kawo muku wasu girke-girke masu armashi da fatan kun ji daɗinsu. A wannan mako kuma ga wasu girke-girke da muka kawo muku da bun sha kuma kamar haka:

 1. Yadda ake lemon karas da lemon zaƙi

A yau za mu nuna muku yadda ake lemon karas haɗe da lemon zaƙi domin shan ruwa. Tare da fatan za a gwada wa mai gida.
Abubuwan da za a bukata:
Karas
Lemon zaki
Sukari
Filebo
Kankara

Yadda ake haɗawa:

A kankare karas a wanke, a kuma yayyanka shi ƙanana a ajiye a gefe.
A wanke lemon zaƙi sannan a ɓare shi a cire ƙwallon a zuba a na’urar markaɗe/ bilenda a markaɗe shi.

Sai a zuba su baki ɗaya a ciki tare da ƙanƙara wacce aka dan farfasa ta. Sannan a markaɗa har sai sun yi laushi.

Sai a sa rariyar tata a tace kamar sau biyu. Sannan a ɗauko sukari a zuba da filebo mai ɗanɗanon lemo.

Sai a yi ta gaurayawa har sai sukarin ya narke, sannan a ɗauko tsaftataccen mazubi a zuba a ciki sannan a sa a gidan sanyi.

Bayan an ci abu mai dumi ne ya kamata a sha wannan haɗin, domin yin buɗa baki da abu mai sanyi sosai na haifar da matsalar lafiya. Don haka sai a kula.

 1. Yadda Ake Alalar Shinkafa

Yanzu za mu kawo muku bayani dalla-dalla kan yadda ake dafa alalar shinkafa, dafa farko har zuwa ƙarshe.

Ga bayani dalla-dalla, daga farko har ƙarshe, kan yadda ake dafa alalar shinkafa.

Kayan haɗi:

Shinkafar tuwo
Nama ko kifi
Man gyadda
Manja
Tattasai
Attarugu
Albasa mai lawashi
Kori
Thyme
Ƙwai
Magi
Gishiri

Yadda ake haɗin:

A wanke shinkafa a shanya ta bushe, sai a niƙa ta a a tankaɗe.
Sannan a samo roba mai zurfi a zuba garin shinkafar a cikin sai a zuba ruwa a kwava kamar kwaɓin ƙullun ƙosai.
A yayyanka dafaffen ƙwai a zuba a ciki.
Sannan a zuba dakakken kayan miya, sai a yayyanka albasa da lawashi ƙanana a ciki.
Daga nan sai a zuba kayan ɗanɗano da man gyadda da man ja dai-dai yadda ake buƙata.
Daga nan sai a marmasa nama ko kifi a zuba a ciki, sannan a zuba kori da thyme a juya sosai ƙullun ya haɗu sosai.
Sai a samu kuma gwangwani ko leda a zuba a cikin dai dai yadda ake so.
Sai a sanya tukunya a wuta sai a zuba ruwa a ciki.
Idan ruwan ya tafasa sai a zuba ƙullin alalen a cikin, a rufe sosai da leda ko gyanyen ayaba.
A bar sa kan wuta har sai ya nuna sosai. Shikenan sai a ci daɗi lafiya. Da fatan za ku jarraba.

 1. Yadda ake tsiren kaza

Abubuwan haɗawa

 1. Tsokar kaza ɗanya
 2. Yajin borkono
 3. Kayan ƙamshi
 4. Maggi
 5. Albasa
 6. Tumatur
 7. Karas
 8. Injin gashin nama
 9. Tsinkayyen tsire

Yadda ake haɗawa:

Da farko dai ki ɗauki yajin barkono ki ki sa a turmi ki kawo kayan ƙamshi da maggi iya ɗanɗanon da zai miki ki sa ki kawo daddawa kaɗan ki sa gishiri kaɗan ki sa ki daka ya daku sosai ajiye a gefe.

Daga nan sai ki ɗauko tsokar kazar ki ki gyara ki yanka su sannan ki faɗaɗa yankan (yankan kamar yanda ake yanka na masu tsire) ajiye a gefe.

Sannan ki ɗauko kwano daban ki sa tsokar kazar ki sa ki kawo yajin ki ki barbaɗa a kai, ki ɗauko albasa ki sa ki ƙara maggi iya ɗanɗanon da zai miki sai ki juya komai ya haɗe da juna sai ki rufe ki sa a firji na ɗan wani lokaci ko ki bar shi ya kwana a ciki idan da dare ki ka haɗa shi.

Daga nan sai ki ɗauko haɗin kazarki sannnan ki kawo tsinken tsire ki ɗauko kina sokawa a jikin tsinkenki kina ajiyewa a gefe ki kunna na’urar gashin naki, idan ta yi zafi, ki kawo haɗin namanki ki jera a kai ki ɗan bar shi na ɗan wani lokaci sai ki juya. Haka za ki yi ta yi har sai ya gasu ki na iya yaryaɗa man gyada da maggi mai ruwa idan kina cikin gasawa dan ya ƙara ɗanɗano.

Daga ƙarshe, da zarar kin ga ya gasu, sai ki sauke sannan ki yanka tumatur, albasa da karas a kai.

Ƙarin bayani:

Idan ki na so gashin naman ki ya dan yi yaji za ki iya idan ya yi rabin gasuwa sai ki sauke ki zuba yajin barkono ki a faranti ki sake baɗe naman da shi, sai ki sake mayarwa a kai ki ƙarasa gasawa. A ci daɗi lafiya.

To masu karatu a nan za mu yi bankwana, sai wani makon kuma idan rainya kai za mu zo muku da wasu girke-girken masu ƙayatarwa. Allah ya karɓi ibadunmu.