Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau
’Yan ta’addan masu tayar da ƙayar baya sun mamaye yankin Samaru da ke Gusau, babban birnin jihar Zamfara, inda suka yi garkuwa da ɗimbin masu gudanar da ibadar Sallar Tahajjud da tsakar daren ranar Talata.
Mazaunin yankin da ya nemi a sakaya sunansa ya shaida wa wakilinmu cewa ‘yan bindigar sun kewaye masallatan da misalin ƙarfe 1:30 na daren yau Talata, inda suka far wa masu ibada a cikin masallacin tare da yin garkuwa da dama daga cikinsu.
“Kamar yadda nake magana a yanzu, har yanzu ba mu kai ga tantance adadin waɗanda aka yi garkuwa da su a lokacin da lamarin ya faru ba amma zan iya shaida muka cewa yawancin mutanenmu da suka haɗa da maza da mata abin ya shafa,” in ji shi.
A cewarsa, ‘yan bindigar sun kai farmaki unguwar ne a kan babura ɗauke da muggan makamai inda suka nufi masallacin kai tsaye suka yi awon gaba da mutanen.
Idan dai za a iya tunawa, a makon da ya gabata ne ‘yan bindigar suka ƙaddamar da irin wannan hari a kan masu ibada a gundumar Keta da ke ƙaramar hukumar Tsafe ta jihar Zamfara inda suka kashe babban limamin masallacin tare da yin garkuwa da da dama yayin harin.
Wakilinmu ya ruwaito cewa, yankunan Damba da Mareri da Tsauni da kuma Samaru da ke Gusau a jihar sun zama wani wuri inda ‘yan bindiga ke kai wa jama’a hari ba dare, ba rana.
A halin da ake ciki, ƙoƙarin jin ta bakin Jami’in Hulɗa da Jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Asp. Yazid Abubakar da wakilinmu ya yi ya ci tura a lokacin haɗa wannan rahoto.