An gano gawar DCP a gidansa a Oyo

Daga BASHIR ISAH

An gano Mataimakin Kwamishinan ‘Yan Sanda (DCP), Gbolahan Olugbemi, kwance a mace a gidansa da ke Ogbomosho, Jihar Oyo.

MANHAJA ta tattaro Olugbemi, wanda ke aiki da rundunar ‘yan sanda ta Jihar Legas, ya tafi gida ne don yin hutun Easter.

An ce mutuwar jami’in cike take da mamaki da ruɗani wanda hakan ya jefa jami’an sashen bincike na FCID na Legas cikin halin jimami.

Majiyarmu ta rawaito cewa, Kakakin FCID, ASP Aminat Mayegun, ta ce za su gudanar da cikakken bincike domin gano dalilin mutuwar jami’in.

Majiya ta kusa da FCID ta ce za a gayyato wasu mutane don amsa tambayoyi kan batun.