Saƙo zuwa ga iyayen gida

Daga FATIMA GARBA DANBORNO

Saƙona zuwa ga mata shi ne, su rage dogon buri. Su gane auren mai kuɗi ba shi ba ne ƙarshen auren ba. Idan har suka ce sun dage sai mai kuɗi, ƙarshe sai kin ga an zo ana danasani.

Su yi iya yinsu su dage da addu’a babu dare babu rana, akan Allah ya yi masu zaɓi da mafi alkhairi. Sau tari auren wani mai kudin ba alkhairi ba ne.

Amma daga lokacin da mace ta kai goshinta ƙasa ta yi addua akan Allah ya yi mata zaɓi da miji na gari mai tsoron Allah, mai ibada. Rokar mai rufin asiri ba laifi ba ne.

Sannan a yayin addu’ar ya zama dole yarinya ta cire kowa a cikin zuciyarta. Muddin aka bi hanyoyin nan insha Allahu ba za a taɓe ba.

Saboda samarin sun gane ‘yan matan suna son rayuwar ƙarya, shiyasa suma suke zuwa suna aron motoci da suturu suna zuwa suna yi wa budurwa ƙarya. Sai an yi aure azo ana ganin ba daidai ba.

Wani ma idan ya gane kwaɗayin budurwar sai ya yi amfani da wannan damar ya yaudareta ya biya buƙatarsa.

Ina son ‘yan mata su gane, a yanzu yaudara ta canza salo. Idan saurayi ya zo gidanku kunyi soyayya bai sanki a ɗiya mace ba, ina ganin ya taimake ki, kuma bai yaudareki ba. Idan kuwa ya gama sanin wajenki da cikinki, wannan ita ce babbar yaudara. Irin wannan nau’in yaudarar ita muke kira da babbar yaudara.

Shi ya sa mafi yawancin lokuta muke raba yaudara kashi biyu. Akwai wanda zai shiga jikinki sosai, ya cusa maki soyayyarsa, sai kowa ya amince zai aure ki, sai ya gudu. Ƙila kuma yana da dalilinsa na guduwan.

Sai kuma babban, wanda ya fi kowanne zama hatsari a cikin rayuwar yarinya, wato wanda zai lallaɓa ki ya gama da ke, sannan ya zagaya ya auri kimtsattsiya. Ko da kuwa shi ne namiji na farko da ya fara saninki bana jin zai taɓa yarda da ke.

Idan an sami mijin ya fito kuma, dan Allah ‘yan mata mu ajiye bidi’a da dagewa akan sai ango ya yi abinda bai da halin yinsa. Duk abin da ya kawo a karɓa da haƙuri. Idan miji ya ce bayason shagulgulan biki sai a haaura, tunda dama can addini bai yarda da su ba.

Allah ya sa mu dace.