Duniyar marubutan Hausa ta girgiza bisa rasuwar Marubuci Bello M. Bello

Daga ADAMU YUSUF INDABO a Kano

Fitaccen matashin marubucin littattafai da fina-finan Hausa, kuma jarumi a masana’antar fina-finan Hausa ta Kannywood, wato Bello M. Bello ya koma ga Mahaliccinsa a daren Talatar da ta gabata (26, 10, 2021). Marigayi Bello M. Bello ya rasu ne a dalilin ciwon ciki da ya kama shi jim ka]an bayan ya yi sallar Magriba, kuma nan take, ya ce ga garinku nan. Ya rasu a gidansa dake cikin garin Ringim ɗin jahar Jigawa, kuma an yi jana’izarsa a washegari ranar Laraba 27, 10, 2021 da misalin ƙarfe takwas na safe.

Marigayi Bello M. Bello, ya rasu yana da shekaru 34 a duniya, ya bar mace ɗaya da ‘ya’ya uku.

Kafin rasuwar tasa, marigayi Bello M. Bello shi ne sakataren ƙungiyar marubutan Jigawa, ‘Jigawa State Writers’ (JISWA). Kuma shi ne mataimakin shugaba na ƙungiyar ‘Arewa Authors Forum’ reshen jahar Jigawa. Daga cikin littattafan da marigayi Bello M. Bello ya wallafa akwai: Sai na aure ta, Ba sai na furta ba, Na amince zan jira ka, Wata biyu da aurena, Bashin iyaye, A dalilinki, da dai sauransu. Sannan yana cikin marubutan fim ɗin nan mai dogon zango na ‘Wuf’ kuma jarumin fim ɗin, Saurayin Hajiya.

Allahu Akbar! Allah Ka ji }an marubuci Bello M. Bello, Ka karɓi shahadarsa. Ya Allah, ka sada shi da masoyinsa shugabanmu, Annabi Muhammadu (S.A.W.) Ameen. A ƙarshe, muna nema masa yafiya a wajen ‘yan uwa da dukkan abokan mu’amala da kuma addu’a gare shi, Allah Ya gafarta masa, idan tamu ta zo, Ya sa mu cika da Imani Ameen.

Alaƙar Marigayi Bello M. Bello da marubuta:
Marigayi Bello M. Bello, mutum ne mai kyakkyawar mu’amala da kowa, wanda dukkan marubutan da suke hulɗa da shi ke yabon halayensa ta kowacce fuska. Ba shi da hayaniya, ba a jayayya da shi balle har ta kai ga musu ko ƙure. Kuma ya ɗauki duk wani marubuci ɗan uwa ne gare shi, walau babba ko ƙarami. Kuma ko bai san mutum ba, suka haɗu ya ji marubuci ne, to yanzu ne zai saki jiki da shi ya mu’amalance shi kamar dama can sun saba. Saboda Muhammad Bello sam ba shi da wuyar sabo. Don haka kowa yake nasa. Wannan ta sa a kafatanin marubuta babu mai zunɗen sa balle ya aibata shi. Muhammad Bello ba shi da ƙullaci, ba shi da abokin rigima, ba ya ba wa kansa ma lokacin da zai yi faɗi-in-faɗa da kowa.

Wannan ya sa jimillar marubuta suke yabonsa, kuma ta sa rasuwarsa ta bugi duk wani wanda ya san shi. Domin daga lokacin rasuwarsa, har i zuwa lokacin da muke haɗa wannan rahoton, marubuta daga sassa daban-daban na duniya na ta rubuce-rubuce ne a yanar gizo maƙale da hotunansa suna ta yabon halayensa da ɗabi’unsa, da kuma nuna alhini. Yayin da wasu kuma suke ɗaukar hanya zuwa garin Ringin ɗin don yi wa iyali da danginsa gaisuwa. Yayin da wasu ma sammako suka doka zuwa garin don su samu jana’zarsa, irin su Marubuci Ayuba Muhammad Ɗanzaki tare da Hammad S. Giɗaɗo da kuma Sulaiman Sid da suka tashi daga jahar Kano, sai kuma Hashim Abdallah daga Malam-madori.

Shaidar da Marigayi Bello M. Bello ya samu daga ‘yanuwa marubuta:
Kamar yadda aka saba ne, a duk lokacin da wani mutumin kirki ya rasu,  za a ji danginsa, da abokansa, da maƙotansa, da abokan mu’amalarsa, da duk wani wanda ya san shi suna kwararo masa addu’ar nema masa rahama da kuma yabon halayensa da kyawawan ɗabi’unsa. To hakan ne ta faru bayan rasuwar marubuci Bello M. Bello. Domin kusan a ce marubuta dake ta’ammali da yanar gizo musamman dandalin abokai na fesbuk. Marubuta suna ta rubutu ne a shafukansu, suna yabon halayensa da kuma yi masa addu’a.

Daga cikinsu akwai Marubuci Hashim Abdallah Malam-Madori, wanda shi ne shugaban Ƙungiyar Marubutan Jigawa ‘Jigawa State Writers’, inda ya ambaci marigayin da cewa: “Ɗan gwagwarmaya ne, mai yi tsakani da Allah, ɗan kishi kuma mai addini.”

Yayin da ita ma fitacciyar marubuciya Jamila Umar Tanko (JUT) ta kira shi da “Mutumin kirki, mai son mutane.” Fasihiyar marubuciya kuma shugabar gidauniyar ‘Creative Helping Needy Foundation’ Hajiya Fauziyya D. Sulaiman cewa ta yi: “Matashi mai ƙaunar iyalinsa da iyayensa, kuma jajirtacce.”

Marubuci Muhammad Lawan Prp, a cikin wani dogon rubutu da ya wallafa a shafinsa na Fesbuk ya ke cewa: “Na same shi mutum mai kamala da nagarta, mai haƙuri da juriya da jajircewa a kan duk abinda ya sa gaba a rayuwarsa. Yana darajta rubutu da ahalinsa. Yana mutumta basirar mutum komai ƙanƙantarta, ba shi da ɗagawa balle girman kai.” Ita ma haziƙar marubuciya kuma shugabar gidauniyar ‘Women Children Dream Foundation’ Hajiya Umma Sulaiman ta yabe shi da cewa: “Yaron kirki, mai girmama mutane, nutsattse, mara hayaniya.”

Yayin da aboki marubuci Zubairu M. Balannaji ya ke cewa: “Hakika na daɗe ban ji rasuwar da ta kiɗima ni kamar taka ba. Allah Ya kyautata makwancinka, Ya tallafi yaran da ka bari.”

Shi ma marubuci kuma babban sha’iri Amb. Ibrahim Adam Ɗansarauta, wanda shi ne shugaban ƙungiyar marubutan Arewa ta ‘Arewa Authors Forum’ reshen jahar Katsina, cikin rubutunsa da ya bayar da labarin haɗuwarsa da marigayi Bello M. Bello ya yabi halayensa da kamar haka: “A ranar Juma’ar da muka sauka Kano don gudanar da bikin ƙannen Balannaji, mun yi ta hidima tare wanda ranar ne muka fara magana da shi, amma sai na ga ya  ɗauke ni tamkar ɗanuwa na jini. Duk da cewa, akwai marubuta da yawa wanda ban sani ba a gurin, amma sai shi ya zama zakaran gwajin dafi wanda shi kaɗai muka ƙulla alaƙa mai kyau da shi, har muka yi musayar lamba kafin wayewar gari.

Wallahi na ji wannan rasuwar domin ina tunawa da irin yadda muka yi zaman mutunci da Bello. Ina yi ma ka fatan kasancewa kusa da masoyinka Annabi Muhammadu (SAW). Allah ya gafarta maka amin.”