Coca-Cola da Pepsi sun fi gurɓata muhalli a Duniya – Bincike

Wani rahoton ƙwararru ya bayyana kamfanin lemun kwalba na Coca-Cola a matsayin wanda ya fi gurɓata muhalli a duniya, inda takwaransa na Pepsi ke biye da shi.

Rahoto ya gano cewa, robobin da waɗannan kamfanoni ke zuba lemunsu a ciki, sun karaɗe sassa da dama na duniya a matsayin shara.

A yayin tattara alƙaluman binciken, sama da mutane 11,000 suka sadaukar da kansu a ƙasashen duniya 45 wajen aikin tsaftace gaɓar tekuna tare da kwashe tarin sharar robobin da waɗannan kamfanoni ke samarwa.

Wasu bayanai na cewa, an tattara sharar robobi sama da 330,000 bayan an yi amfani da su sau ɗaya tal, kuma robobin Cocoa-Cola ke kan gaba, sannan na Pepsi da ke biye da shi, yayin da robobin Unilever ke a matsayi na uku.

A karo na huɗu kenan a jere da Coca-cola ke kasancewa kan gaba a jerin kamfanonin da robobinsu ke gurvata muhalli, amma a karon farko kenan da Unilever ya haura mataki na uku.

Wannan rahoton da aka fitar na zuwa ne mako guda gabanin fara babban taron sauyin yanayi na COP26 a birnin Glascow, inda ƙasashen duniya za su sake nazartar hanyoyin magance matsalar ta sauyin yanayi da ke barazana ga halittun duniya.