Matsalolin ilmi a Jihar Kano

Gwamna Ganduje

Daga FATUHU MUSTAPHA

Ilmi na cikin vangarorin rayuwa da ya zamewa ɗan Adam tilas ya ba shi kulawa ta musamman. A yau Ƙasar nan tana fuskantar manyan matsaloli kama daga matsalar tsaro da a kullum ke ƙara ta’azzara, zuwa matsalar fatara da talauci, lalaci da jahilci da kuma karyewar tattalin arzikin ƙasa, wanda a ka fara sa ran zai iya farfaɗowa nan da wasu lokuta masu zuwa.

Babu inda matsalolin nan suka fi nunawa kan su irin a Arewacin Nijeriya. Inda anan ne aka fi yawan yaran da basa zuwa makaranta, yawan yaran da basa cin jarabawar gama sakandire wato waec da NECO. Baya ga matsalar kwararowar almajirai daga sassa da dama na ƙasar nan zuwa manyan birane a yankin wanda hakan ke ƙara janyo taɓarɓarewar tarbiya da yawaitar laifuka. Wasu masana na ganin wannan na da alaƙa da samuwar ƙungiyoyin addini masu tsattsauran ra’ayi musamman ma Boko Haram, da Ƙala Ƙato da Maitatsine.

Ɗaya daga cikin manyan matsalolin da suka fi ci wa hukumomi a duniya tuwo a ƙwarya game da Arewa shi ne matsalar ilmi kamar yadda muka bayyana a sama. Jihar Kano na cikin jihohin da wannan matsala a kullum take ƙara lalacewa. Masana suna zargin abubuwa da dama da suka janyo jihar ke ƙara samun koma baya a fannin ilmi, duk kuwa da tana cikin jihohi goma masu ƙarfin tattalin arziki a Nijeriya. Haka kuma  ita ce ta ɗaya a yawan jama’a a ƙasar, to amma kuma a fannin ilmi, Jihar na cikin jihohi da suke koma baya a ɓangaren.

A shekarun baya, kusan shekaru 30 da suka gabata, jihar na sahun gaba a wannan ɓangaren, musamman in aka yi la’akari da ta zama a wurin ta wasu jihohin ke ɗaukar samfur, na yadda za a ciyar da ilmi gaba. Jihar dai ita ta fara ƙirƙiro da tsarin Hukuma Kula da Ilmin Manya a Arewacin Nijeriya. Haka ita ta fara kafa  Hukumar Kula da Ilmin Kimiyya kafin sauran jihohi su koya a wurin ta. Wanda haka ya taimaka matuƙa gaya wurin zaburar da matasa su rungumi ilmin Kimiyya da Fasaha a duk faɗin jihar.

A zamanin Gwamna Abubakar Rimi ma 1979 – 1983 ta taɓa zuwa da wani tsarin makarantun sana’a (vocational school), saboda ɗaliban da basu ba ƙwaƙwalwar karatu mai zurfi su koyi sana’a. Hakan kuma ya taimaka ƙwarai wurin samar da ayyukan yi ga ɗimbin matasa da ba su samu damar cin jarabawar shiga makarantun gaba da sakandire ba.
A zamanin gwamnatin Kwankwaso da ya yi a karo na biyu 2011 – 2015 ma, gwamnatin ta kashe biliyoyin nairori domin ciyar da ilmi gaba. Inda aka samarwa da ɗalibai sama da dubu biyu guraben qaro ilmi a ƙasashen waje, da kuma wasu da dama a jami’o’i masu zaman kan su. Baya ga haka kuma an samar da sabbin makarantu daban daban, kama daga na koyon sana’o’i zuwa na ilmin addini da na zamani. Har ma aka buɗe shahararriyar makarantar koyar da Ilmin komfuta nan mai suna Informatics.

To amma bisa ga dukkan alamu, ilmi a Jihar Kano a yau ya samu koma baya matuƙa, a wani bincike da Jaridar Manhaja ta gabatar, ta gano cewa, akwai matsaloli masu tarin yawa a fannin ilmi a jihar. Wannan ya faru ne saboda, halin ko in kula da gwamnati mai ci a yanzu ke nunawa ilmin, matsalar cin hanci da rashawa da ya kunno kai a fagen, rashin isassun kayan aiki, rashin malamai ƙwararru, da dai sauran su.

A wannan makon Jihar ta yi iƙirarin ta maida yara makaranta da yawan su ya kai har miliyan uku da ɗigo huɗu. To amma kuma abin tambaya anan shi ne, shin an samar da kayar karatun da yaran za su koyi abinda ake so su koya? An samar musu da wurin da za su zauna su yi karatun cikin kwanciyar hankali? Shin an baiwa Malaman na su horon da ya dace, ta yadda za su iya ilmantar da yaran? Waɗannan da ma wasu tambayoyi da dama, na cikin tambayoyin da masana suke yi akan wannan.

A cikin shekarar 2020 Gwamnatin Jihar Kano ta shelanta karvo rancen kuɗi har Naira Biliyan 15 domin inganta ilmi da samar da ilmi kyauta. To amma a binciken da mu ka gabatar, ya tabbatar mana da cewa, walau dai dambu ne ya yi yawa, ya zama na baya jin mai, ko kuma akwai lauje cikin naɗi akan wannan rance da aka karɓo.

Wasu Malaman da muka zanta da su, sun koka

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *