Rahoto

Ka ji tsoron Allah, ba Trump ba – Shawarar Sarkin Iwo ga Tinubu

Ka ji tsoron Allah, ba Trump ba – Shawarar Sarkin Iwo ga Tinubu

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Sarkin Masarautar Iwo, wato Oluwo na ƙasar Iwo da ke Jihar Osun, Oba Abdurosheed Akanbi, ya shawarci Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu da ya mayar da hankalinsa wajen tsoron Allah fiye da tsoron kowanne mutum, ciki har da Shugaban Amurka, Donald Trump. Ya ce, idan shugaba Tinubu zai miƙa wuya ga Allah da gaske — wanda shi ne ya halicci Trump — to babu abin da zai tsoratar da shi. Da yake jawabi a bikin shekara-shekara na Olodumare da aka gudanar a garin Iwo a ranar Lahadi, Oluwo ya bayyana cewa garinsu bai taɓa fuskantar yaƙi…
Read More
Wane ne Ted Cruz, sanatan Amurka da ya fara zargin kashe Kiristoci a Nijeriya?

Wane ne Ted Cruz, sanatan Amurka da ya fara zargin kashe Kiristoci a Nijeriya?

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Tun bayan maganganun Shugaban ƙasar Amurka, Donald Trump, wanda ya laƙanci Nijeriya a matsayin “ƙasa mai matsalar cin zarafin addini” tare da yin barazanar aikewa da sojojin Amurka ƙasar, cece-kuce ya kunno kai a kafafen yaɗa labarai da kuma dandalin sada zumunta. Sai dai kafin wannan rikici ya yi zafi, wani fitaccen sanata na Amurka, Ted Cruz, shine ya daɗe yana rura wutar wannan tuhuma ta ‘kisan Kiristoci’ a Nijeriya tuni, yana mai cewa, gwamnati na nuna son rai da wariyar addini. Wannan rahoto ya kawo tarihin mutumin da ya fara iza wutar zargi daga nisan…
Read More
Maguzawa daban Muguzanci daban

Maguzawa daban Muguzanci daban

Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA Haƙiƙa akwai jama’a da su ke zama lafiya a matsayin maguzawa a garuruwan Hausawa. Kama daga yankin Malumfashi a jihar Katsina, zuwa wajajen Sumaila a jihar Kano da ma yankunan jihar Jigawa har ma cikin ƙasar Gobir; a na samun maguzawa da ke zaune da iyalinsu lafiya kuma sun fi zama a ƙauyuka. A gefe guda yayin da maguzawa ke zama al’umma da ke rayuwa irin ta gargajiya da zabar rashin shin shiga Musulunci, akwai kuma wata ɗabi’a ta maguzanci da ba lallai sai a waɗannan yankuna da na lissafa ba. Za a iya samun maguzanci…
Read More
Kwalliya: Garin neman gira za a rasa ido 

Kwalliya: Garin neman gira za a rasa ido 

Tare da BILKISU YUSUF ALI A yau, batun kwalliya ya zama ɗaya daga cikin muhimman al’amura da suka shafi rayuwar mata, musamman matasa. Duk da cewa kwalliya wani nau’i ne na bayyana tsafta da ƙawata kai, an gano cewa akwai ƙaruwa mai yawa wajen amfani da kayan kwalliya masu haɗari, musamman na fata (skin lightening creams). Wannan lamari ya janyo damuwa a tsakanin masana lafiya da manazarta a fannin zamantakewa da lafiya. Wannan nazari za mu  tattauna matsalar amfani da kayan kwalliya masu haɗari, binciken masana, da kuma muhimmancin kwalliya ga mace idan an yi ta daidai. Matsalar kayan kwalliya…
Read More
Tarihin zuwan karatun boko a Nijeriya

Tarihin zuwan karatun boko a Nijeriya

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD A yau idan ka zagaya makarantu a Nijeriya, daga garuruwa har ƙauyuka, za ka ga yara da manya suna koyon karatun boko — wanda ke nufin tsarin ilimin zamani da Turawa suka gabatar. Amma kafin wannan tsarin ya karɓu, akwai doguwar hanya da tarihi mai cike da abubuwan mamaki da al'adu daban-daban da suka taka rawa wajen samuwar karatun boko a Nijeriya. Farkon zuwan Turawa da asalin karatun boko: Karatun boko ya samo asali ne daga tsarin ilimi na Turawan mulkin mallaka, musamman na Birtaniya, waɗanda suka mamaye sassan Nijeriya tun ƙarshen ƙarni na 19. Kafin…
Read More
Yadda haƙowa da cinikin zinare ke ƙarfafa ta’addanci a Arewa maso Yamma

Yadda haƙowa da cinikin zinare ke ƙarfafa ta’addanci a Arewa maso Yamma

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD An ƙiyasta cewa, Nijeriya tana yin asarar sama da Dala biliyan tara duk shekara saboda haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba — inda kaso mafi yawa ya ta’allaƙa ne da haƙar zinariya. Wani bincike da jaridar Daily Trust ta gudanar ya gano cewa babbar kashi daga cikin zinariyar da ake haƙowa a Arewa maso Yamma tana komawa hannun masu ta’addanci don su riƙa samun kuɗaɗen sayen makamai ne. A ƙarƙashin ƙasar Zamfara mai arzikin zinariya, wani ɗan bindiga mai suna Kachalla Mati, wanda ya gaji gawurtaccen shugaban ’yan ta’adda Halilu Sububu, ana zargin yana tara fiye…
Read More
Majalisar Zartarwar Kano ta amince da kashe Biliyan N19 domin ayyuka masu muhimmanci

Majalisar Zartarwar Kano ta amince da kashe Biliyan N19 domin ayyuka masu muhimmanci

Daga RABIU SANUSI a Kano Majalisar Zartarwar Jihar Kano, ƙarƙashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf, ta amince da kashe Naira biliyan 19.02 domin aiwatar da muhimman ayyuka a fannoni daban-daban na cigaban tattalin arziki da jin daɗin al’umma. Kwamishinan yaɗa labarai da harkokin cikin gida na Jihar Kano, Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya ne ya bayyana haka yayin da yake ma Manema Labarai ƙarin haske bayan kammala zaman majalisar karo na 33 da aka gudanar a fadar gwamnatin Kano, ranar Asabar, 1 ga Nuwamba, 2025. A cewar Waiya, majalisar ta tattauna muhimman batutuwa da suka shafi mulki, ci gaban tattalin arziki,…
Read More
Zuwa ga maza masu dukan mata

Zuwa ga maza masu dukan mata

A cikin al’ummar da take kiran kanta mai imani, mai al’ada da ɗabi’a, abin takaici ne yadda muke ƙara ganin yawaitar wani abin kunya da ke neman zama ruwan dare — dukan mata. Wannan ɗabi’a ta zalunci ta zama abin da ke lalata iyali, ke haifar da zubar hawaye, da kuma rage darajar aure a idon jama’a. A yau, da dama daga cikin maza sun ɗauki duka a matsayin hanyar gyara mata, ko kuma hujjar nuna iko. Amma gaskiyar magana ita ce: duk wani namiji da ke dukan matarsa ba jarumi ba ne, kuma ba shugaba nagari ba ne. Domin…
Read More
Manufarmu ita ce cusa ɗa’a da kishin ƙasa ga ’yan Arewa – AIRLIN

Manufarmu ita ce cusa ɗa’a da kishin ƙasa ga ’yan Arewa – AIRLIN

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Wata ƙungiyar mai zaman kanta da ke wayar da kan al'ummar Arewacin Nijeriya kan muhimmanci yin zaɓe, cusa ɗa'a, nuna kishin ƙasa da kyautata tarbiyya mai suna 'Adɓocacy for Integrity and Rule of Law Initiatiɓe' (AIRLIN) ta yi kira ga ’yan Nijeriya musamman mazauna yankunan Arewa da su shiga cikin harkokin zaɓe ta hanyar amfani da ’yancin da tsarin mulki ya ba su da kuma zaɓen shugabanni nagari. Kodinetan ƙungiyar na ƙasa, Alhaji Muhammad Ibrahim Gamawa ya yi wannan kiran ne a yayin bikin ƙaddamar da ko’odinetocin jiha da ƙananan hukumomin Jihar Kaduna a Arewa House,…
Read More
Kasuwar Mile-12 ta zarce sa’o’inta na ƙasashen Afrika – Bala Gozaki

Kasuwar Mile-12 ta zarce sa’o’inta na ƙasashen Afrika – Bala Gozaki

Daga DAUDA USMAN a Legas Shugaban sashen kasuwancin dankalin turawa na kasuwar Mile 12 International Market da ke Legas, Alhaji Bala Magaji Gozaki, ya bayyana cewa kasuwar Mile 12 ta zama babbar kasuwa a Nijeriya da ma Afrika baki ɗaya, bisa yawan al’ummar ƙasashen waje da ke gudanar da cinikayya a cikinta. Alhaji Bala Magaji, wanda asalinsa daga karamar hukumar Kafur ta jihar Katsina ne, ya ce kasuwar ta kai matsayin da za a iya cewa “kasuwa ta ƙasa da ƙasa” saboda irin ci gaba da haɓakar da take samu a kowanne bangare, musamman wajen jawo ‘yan kasuwa daga ƙasashen…
Read More