Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Sarkin Masarautar Iwo, wato Oluwo na ƙasar Iwo da ke Jihar Osun, Oba Abdurosheed Akanbi, ya shawarci Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu da ya mayar da hankalinsa wajen tsoron Allah fiye da tsoron kowanne mutum, ciki har da Shugaban Amurka, Donald Trump.
Ya ce, idan shugaba Tinubu zai miƙa wuya ga Allah da gaske — wanda shi ne ya halicci Trump — to babu abin da zai tsoratar da shi.
Da yake jawabi a bikin shekara-shekara na Olodumare da aka gudanar a garin Iwo a ranar Lahadi, Oluwo ya bayyana cewa garinsu bai taɓa fuskantar yaƙi ko mamaya ba, saboda sun sanya tsoron Allah a gaba.
“Tinubu zai ci nasara idan ya miƙa dukkan yabo ga Allah Maɗaukaki. Ya kamata ya ƙara mayar da hankali wajen gode wa Allah fiye da yadda yake yi a yanzu. Idan dukkanmu muka koma ga Allah, babu abin da zai zama abin tsoro. A nan Iwoland ba mu jin tsoron kowa, ba mu jin tsoron makaman nukiliya, ba mu jin tsoron Trump. Don haka, Tinubu ma bai kamata ya ji tsoron Trump ba — ya kamata ya ji tsoron Allah. Wannan ne ya sa ba a taɓa cin ƙasar Iwo da yaƙi ba,” inji shi.
Oluwo ya kuma bayyana ‘la’anar gado’ a matsayin babban cikas ga ci gaban mutane, inda ya ce bikin Olodumare bana an shirya shi ne domin addu’ar kawar da irin wannan la’ana daga ƙasa.
“Bikinmu na kowacce shekara na nufin yin addu’a ga Allah domin samun sauyi. A bana muna roƙon Allah ya tsarkake ƙasarmu daga la’anonin gado. Ni sarki ne da Allah ya zaɓa domin jagorantar wannan addu’a. Ita ce addu’ar da za ta kawar da duk wata la’ana,” inji shi.
Ya kuma yi kira ga sauran sarakunan gargajiya a faɗin yankin Yarbawa da su yi koyi da shi ta hanyar wakiltar Allah a doron ƙasa, maimakon bautar gumaka ko sauran halittu.
“Dukkan sarakunan gargajiya su sani cewa fadarsu mallakin Allah ne, kuma wajibi ne su kasance wakilan Allah a duniya, ba wakilan gumaka ba. Allah kaɗai ne ke naɗa sarki,” inji Oluwo.
