
A ranar Juma’a ne Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani ya gabatar da nasarorin da gwamnatinsa ta cimma tare da bayyana sabon taswirar ci-gaba a yayin taron tattaunawa da jama’a kan kasafin kuɗi na 2026.
Uba Sani ya jaddada ƙudirinsa na tafiyar da gwamnati mai adalci, daidaito, da kuma zuba jari mai ma’ana wanda zai kawo sauyi kai tsaye ga al’ummomi a faɗin jihar.
A ɓangaren gina manyan titina da ci-gaban karkara, Gwamnan ya bayyana cewa an kammala gina titina sama da kilomita 785 a mataki na ɗaya, yayin da ake cigaba da aikin wasu kilomita 550 a mataki na biyu a dukkan ƙananan hukumomi 23 na jihar.
Waɗannan ayyuka na da nufin inganta hanyoyin sadarwa, farfaɗo da tattalin arziƙin karkara, da kuma sauƙaƙa zirga-zirga a faɗin jihar.
Ya ƙara da cewa, gwamnati na shirin fara aikin jirgin ƙasa na zamani da samar da motocin safa fasa na zamani (BRT), wanda ka iya mayar da Kaduna jiha ta biyu a Nijeriya da ta rungumi irin wannan tsarin sufurin.
A fannin kiwon lafiya, Gwamna Sani ya jaddada cewa an inganta cibiyoyin kiwon lafiya na farko guda 200, lamarin da ya sanya Kaduna ta zama jiha mafi kyawu a Arewa maso Yamma da kuma ta biyu a fadin kasa wajen gudanar da harkokin kiwon lafiya a matakin farko.
Haka kuma ya bayyana ci-gaban da aka samu wajen gyara tare faɗaɗawa, da samar da kayan aiki ga asibitocin gwamnati 32, inda 14 daga ciki aka kammala su.
Wannan ya tabbatar da karin damar samun ingantacciyar kiwon lafiya musamman ga al’ummomi masu nisa da birane.
Kazalika, a ɓangaren taimaka wa manoma da inganta tattalin arziƙi, Gwamnan ya ce gwamnati ta raba motoci masu ɗaukar kaya 900 na taki ga ƙananan manoma fiye da 200,000, tare da rattaɓa hannu kan yarjejeniyar zuba jarin kaji na Dala miliyan 450 da gwamnatin ƙasar Sin.
Kaduna na fitowa a matsayin cibiyar koyon sana’o’i a Nijeriya, inda matasa 90,000 ke koyon kwarewa daban-daban, yayin da 32,000 suka amfana da horo na kasa da kasa.
Shi ma, Kwamishinan Tsare-tsare da Kasafin Kuɗi na jihar Kaduna Mukhtar Ahmed Monrovia, ya bayyana cewa an ware Naira biliyan 80.2 a cikin kasafin 2026 domin biyan bashin da aka gada daga gwamnatoci da suka gabata.
Ya ce, duk da nauyin bashin ciki har da na ƙasashen waje har zuwa shekarar 2026 Gwamna Sani bai ci bashin kobo guda ba tun da ya hau mulki, yana dogaro da ingantaccen tsarin tara kudaden shiga da tsare-tsaren kashe kudi.
Haka kuma ya sanar da sabbin tsare-tsaren kula da kudaden gwamnati, inda ya kawo karshen tsarin da ‘yan kwangila ke neman alfarma kafin biyan su.
Daga yanzu, za a biya kwangila kai tsaye bayan amincewa da takardunsu.
Kasafin Kuɗin 2026: Mai taken Zuba Jari da Tallafa wa Jama’a:
Gwamna Sani ya gabatar da kasafin naira biliyan 985.9 na shekarar 2026 karin kaso 24.73% daga na shekarar 2025.
Kasafin ya ware kashi 71% naira biliyan 699.7 ga ayyukan ci gaba, yayin da kashi 29% wato naira biliyan.2 ga kudaden gudanarwa. Muhimman sassa sun hada da:
Ilimi kashi (25%)
Ayyukan Gine-gine kashi (25%)
Lafiya kashi (15%)
Noma kashi (11.5%)
Tsaro da Gina Zaman Lafiya kashi (6%)
Tallafin Jama’a kashi (5%)
Muhalli & Sauyin Yanayi kashi (4%)
Sauran kashi (8.5%)
Gwamnan ya jaddada matsayin Kaduna a matsayin zuciyar siyasa a Arewacin Nijeriya. Ya mika godiya ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu bisa zabar Kaduna a cikin masu cin gajiyar zuba jari na dala miliyan 450, kana ya yi godiya ga kasar Sin bisa goyon bayan da take bai wa jihar.
Gwamna Sani ya yi alƙawarin ci-gaba da hanzarta shi, aiwatar da adalci da gaskiya, tare da tabbatar da cewa kowane dan Kaduna zai ji tasirin ci-gaban da ake samu yayin da jihar ke matsawa gaba cikin shekarar 2026 da ma bayan haka.



