
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
A jiya Juma’a Mayaƙan ƙungiyar ISWAP suka yi kwantan-ɓauna akan tawagar motocin sojoji a Jihar Borno, inda suka halaka jami’an haɗaka na CJTF da wasu sojoji.
Baya ga haka ne aka nemi ɗaya daga cikin sojojin mai muƙamin janar aka rasa.
Harin ya auku ne da misalin ƙarfe 5 na yamma a kusa da Sabon Gari akan hanyar Damoa zuwa Biu, a lokacin da sojoji suke rakiyar wani babban jami’i da makamai a wani yanki mai hatsari a Arewa maso Gabas.
Majiyoyin tsaro da na al’umma sun tabbatar wa manema labarai cewa mayaƙan na ISWAP sun fake ne acikin jeji ta kusa da wajen wucewar sojojin, inda suka buɗe musu wuta yayin da suka kusanto yankin, lamarin da ya haddasa ba-takashi tsakanin ɓangarorin biyu.
Wani mamban CJTF ya ce, ƴan ta’addar sun halaka sojoji guda shida da ƴan CJTF takwas da kuma yi awon-gaba da baburan jami’an tsaron.
Haka kuma, wani mazaunin Damboa ya bayyana cewa tawagar ta bar garin ne da misalin ƙarfe 2 na rana a wasu motocin Hilux guda biyu, motocin yaƙi biyu da kuma baburan masu yawa gabanin su kutsa cikin jeji.
Kazalika, wani mamban CJTF ya ce babban abin takaicin shi ne rashin ganin Kwamandan wata Birget, wanda shi ke jagorantar su a lokacin da al’amarin ya auku.
Saidai ba a samu ji ta bakin rundunar sojojin Nijeriya ba a yayin kammala haɗa rahoton domin bada ƙarin bayani akan al’amarin.
