Taron PDP: ‘Yaƴan jam’iyya sun cika Ibadan duk da umarnin kotu na hanawa

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Al’umma sun cika filin wasa na Lekan da ke Birnin Ibadan a Jihar Oyo, yayin da babbar jam’iyyar adawa a Nijeriya (PDP) ta fara shirye-shiryen gudanar da Babban taronta na ƙasa duk da rikicin cikin gida da na shari’a da ake cigaba da fuskanta jagororinta.

Rahotanni sun bayyana cewa tun da misalin ƙarfe 7 na safe ne aka ga taron deliget, jami’an tsaro, ma’aikatan sufuri da magoya baya sun yi cincirindo domin fara taron.

A cewar jaridar NewsPointNigeria, an ga dandazon jama’a a wajen taron, wanda hakan ya sa kwamitin shirye-shirye ya ƙara adadin jami’an tsaro domin kula da taron.

Haka kuma, an samu cinkoson ababen hawa a yankin babbar ƙofar shiga filin, lamarin da ya tilasta wa jami’an sufuri na NURTW aiki kafaɗa-da-kafaɗa da hukumomin tsaro na jihar wajen ganin an tafiyar da harkokin zirga-zirga bisa tsari.

Babban taron ya kuma haɗa jagorori, masu ruwa da tsaki da jiga-jigan ƴan jam’iyyar daga sassan Nijeriya, musamman ganin yadda rikicin cikin gida akan jagoranci, alƙibla da haɗin kan ƴaƴan PDPn ke ƙara ƙamari.

Har yanzu dai jam’iyyar tana nan a rabe gida biyu, wato ɓangaren jagorancin Shugaban riƙo Umar Damagum da kuma na Abdulrahman Muammed, wanda sun bambanta akan matsayar taron na Ibadan.

By Babaji