Ba a yi garkuwa da janar ba a harin ISWAP, inji Rundunar Sojoji

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Rundunar Sojoji ta tabbatar da kai wa dakarun Task Force Brigade na 25 ƙarƙashin jagorancin mayaƙan ISWAP a Jihar Borno da ke yankin Arewa maso Gabas.

Al’amarin ya faru ne a lokacin da jami’an suke kan hanyar dawowa daga wani atisayen da suka yi nasara a Dajin Sambisa, wanda ya yi sanadin mutuwar sojoji biyu da mambobin jami’an sa kai na haɗaka na CJTF su ma su biyu.

Harin, wanda ya auku a ranar Juma’a da misalin ƙarfe 5 na yamma an ƙaddamar da shi ne a yankin Sabon Gari a babbar hanyar Damoa zuwa Biu, wadda ke da hatsari ga matafiya duba da yawan hare-hare da ƴan ta’adda ke kaiwa.

A wata takarda da Darakta yaɗa labaran sojoji na riƙo, Appolonia Anele ta fitar, ta ce sojojin suna aikin sintiri ne domin ba ƙauyukan da ke yankin kariya a Azir Multe da ke Ƙaramar Hukumar Damboa, inda ba su yi aune ba sai suka fara jin harbi daga mayaƙan, waɗanda suka yi kwantan-ɓauna a gefe titin.

Ta bayyana cewa, tawagar sojojin ƙarƙashin jagorancin Kwamandan Birget ɗin, Janar M. Uba suka mayar da martani wanda hakan ya sa mayaƙan suka ja da baya.

A cewarta, sojoji biyu da jami’an CJTF biyu sun rasu yayin arangamar, inda kuma ta miƙa ta’aziyya a madadin rundunar ga iyalan mamatan tare da jinjina wa jarumta da sadaukarwarsu.

Saidai, a yayin haka ne wasu kafafen yaɗa labarai suka baza cewa an yi garkuwa da kwamandan, zancen da rundunar ta ƙaryata da kiran hakan da hanyar ruɗar da al’umma.

By Babaji