
Rundunar ƴan sanda ta tsare Alwan Hassan, Shugaban kungiyar Grassroots Initiative Concept, kwana kaɗan bayan ya zargi Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Barau Jibrin da hana tantance Abdullahi Garba Ramat a matsayin Shugaban Hukumar Kula da Wutar Lantarki ta Kasa, NERC.
Rahotanni sun bayyana cewa an tsare Hassan ne a Sashen Binciken Manyan Laifuka na Rundunar ‘Yansanda, FCID, da ke Abuja bayan ya amsa gayyatar ƴansanda a jiya Juma’a.
Babu cikakken bayani kan ƙorafi ko zargin da ya haifar da wannan gayyata a lokacin da aka samun wannan rahoto.
Hassan, wanda tsohon hadimin shugaban kasa, a kwanan nan yi zargin cewa shugabancin Majalisar Dattawa na yin kafar ungulu ga tabbatar da Ramat, ɗan asalin Kano kuma gogaggen masani a fanninduk da cewa ya yi nasarar hayewa yayin tantancewa tare da samun amincewar Kwamitin Majalisar Dattawa kan Harkokin Wutar Lantarki.
Ya kara da cewa wasu jami’an Majalisar Dattawa sun nemi cin hanci na dala miliyan 10 daga wadanda aka zaba za a naɗa su a shuagabancin NERC kafin a tantance su, zargin da Majalisar Dattawa ta ƙaryata cikin gaggawa, tana mai cewa babu tushe kuma bata suna ne.
