Da Ɗumi-Ɗumi: Tsagin PDP ya amince da Damagum a matsayin tabbataccen shugaba

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Tsagin Babbar Jam’iyyar adawa (PDP) ya tabbatar da Umaru Damagum a matsayin halastaccen shugaba.

An yanke hukuncin ne yayin wani babban taron jam’iyyar na 2025 wanda ake gudanarwa a yau Asabar a filin wasa na Lekan da ke Ibadan a Jihar Oyo.

Hon. Tony Abineri, wato Shugaban jam’iyyar na Jihar Edo tare da masu zaɓe (deliget) guda 3,000 suka gabatar da shi, lamarin da ya samu goyon baya daga Edward Marshal.

Abineri ya bayyana cewa matsayar ta yi daidai da sashe na 32 da kundin dokokin jam’iyyar.

“Ina mai gabatar da ƙudirin gamsuwa da Ambasada Umaru Damagum a matsayin tabbataccen shugaban jam’iyya na ƙasa”, inji Abineri.

By Babaji