
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
A safiyar yau Asabar ne ƴan bindiga suka kashe Alhaji Umar S Fada Moriki wanda fitaccen ɗan siyasa a jihar Zamfara kuma jigo a jam’iyyar APC.
Rahotonni sun ce lamarin ya faru ne wani yanki na babban titin Gusau zuwa Tsafe, a lokacin da yake kan hanyarsa ta zuwa Kaduna daga Gusau.
A wata sanarwa da jam’iyyar APC reshen jihar ta fitar, mai ɗauke da sa hannun sakataren yaɗa labaranta, Yusuf Idris ya ce marigayin ya gamu da ajalinsa ne bayan halartar taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar, wanda Ƙaramin Ministan tsaron Nijeriya, Mohammed Bello Matawalle ya jagoranta.
Marigayin mai shekaru 62 ya taɓa rike mukamin mataimakin shugaban ƙaramar hukumar Zurmi, sannan ya riƙe muƙamin babban darakta a wata hukuma kafin ya zama mataimakin gwamna na musamman akan samar da lantarki a karkara.
Haka kuma, a zaɓukan 2023 da suka gabata ya tsaya takarar ɗan Majalisar Wakilai mai wakiltar ƙananan hukumomin Zurmi da Shinkafi.
Kazalika, ya rayu tare da mata guda uku da ƴaƴa masu yawa.
