Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT), Nyesom Wike, ya bayyana rashin jin daɗunsa kan abin da ya kira da “mamayar sojoji” kan wani fili da ake rikici a kansa a Abuja.
Wike ya kai ziyara kai tsaye zuwa wurin a ranar Talata bayan samun rahoto cewa wasu sojoji sun kori jami’an hukumar raya birane ta FCTA da ke aikin hana gini ba bisa ka’ida ba.
Yayin da yake magana da manema laɓaria bayan faruwar lamarin, Wike ya gargaɗi masu amfani da ƙarfin soja don hana gwamnati aiwatar da doka, yana mai cewa ba zai lamunci irin wannan rashin da’a ba.
Wike ya ce, jami’an sashen kula da raya birane sun je wurin domin aiwatar da umarninsa na hana gini, amma wasu sojoji da ake zargin suna aiki da umarnin tsohon hafsan soja suka kore su.
“Ina ofis aka kira ni cewa sojoji sun mamaye wurin,” inji shi. Ya ƙara da cewa, “Lamarin abin takaici ne sosai.”
Ya ce, ya yi mamaki cewa tsohon babban jami’in soja zai nuna ƙarfi maimakon bin matakan doka da suka dace.
Ministan ya ce, bai fahimci yadda mutum da ya taba riƙe mukamin soja mafi girma zai kasa zuwa ofishinsa domin tattaunawa ba, sai dai ya nemi amfani da soja don tsoratar da hukumomi.
“Ni bana cikin waɗanda za su lamunci barazana,” unji Wike cikin tsawa. “Ba za mu bari rashin doka ya mamaye FCT ba.”
Ya ƙara da cewa, jami’an hukumar raya birane sun buƙaci masu ginin su kawo takardu ko izinin mallaka, amma ba su da ko ɗaya.
Wike ya ce, babu wani tsarin doka da aka bi wajen mallakar filin, domin babu rajista, babu amincewar gwamnati, kuma babu izinin gini.
“Idan muka ci gaba da barin irin wannan rashin doka, yaya sauran ‘yan kasa masu biyayya ga doka za su ji?”
Ya kuma bayyana cewa tuni ya tuntuɓi hafsan tsaron ƙasa da hafsan rundunar sojan ruwa, waɗanda suka tabbatar masa cewa za a magance matsalar cikin lumana.
