Tare da BILKISU YUSUF ALI
A yau, batun kwalliya ya zama ɗaya daga cikin muhimman al’amura da suka shafi rayuwar mata, musamman matasa. Duk da cewa kwalliya wani nau’i ne na bayyana tsafta da ƙawata kai, an gano cewa akwai ƙaruwa mai yawa wajen amfani da kayan kwalliya masu haɗari, musamman na fata (skin lightening creams). Wannan lamari ya janyo damuwa a tsakanin masana lafiya da manazarta a fannin zamantakewa da lafiya. Wannan nazari za mu tattauna matsalar amfani da kayan kwalliya masu haɗari, binciken masana, da kuma muhimmancin kwalliya ga mace idan an yi ta daidai.
Matsalar kayan kwalliya masu haɗari
Amfani da kayan gyaran fata da kwalliya kamar mayuka masu sa haske (bleaching cream) da sabulai masu ƙara fari (whitening soaps) da wasu man leɓe ko janbaki masu haɗari (lipsticks) da masu sinadaran guba ya zama ruwan dare a tsakanin mata. A mafi yawan lokuta, ana amfani da waɗannan kayan domin ƙara haske ga fata, cire tabo ko gyara fuska. Sai dai bincike ya tabbatar da cewa yawancin waɗannan kayan na ɗauke da sinadarai masu illa irin su mercury, hydroƙuinone, corticosteroids, da lead. Wadannan na iya janyo matsaloli kamar:
ƙonewa ko kumburin fata.
Nannaɗewar fata da bayyana jijiyoyi.
ƙarancin kariya daga hasken rana (UV) wanda ke iya haifar da kansar fata.
Guba a cikin jiki (koda da hanta da jijiya).
Canjin launin fata mai ɗaukar hankali da kunyata mutum.
Wasu kayan kwalliya na baka kamar lipsticks na iya ƙunsar sinadarai kamar lead da cadmium waɗanda ke iya shiga jiki a hankali ta hanyar baki, suna janyo matsaloli ga lafiyar kwakwalwa da hanta.Masana daga hukumar lafiya sun bayyana cewa amfani da sinadarai masu haɗari kamar mercury yana iya kai wa ga ciwon koda da sauran cututtuka na ciki.
Wani muhimmin abin lura daga waɗannan bincike shi ne: mace tana amfani da kayan kwalliya ba domin ƙawata kanta kawai ba, amma domin ta dace da ƙa’idar kyawu da al’umma suka gindaya – wato launin fata mai haske da kyau na fuska.
Shawara ga mata
Mata yana da kyau su san cewa ba sai sun yi amfani da kayan kwalliya masu sauya launi ba za su yi kyau ba, akwai hanyoyi da daman gaske da mata za su yi amfani da shi kuma a samu abin da ake nema ba tare da sun cutar da lafiya ba. Akwai matakai da dama da mata za su bi don tabbatar da ingancin abin da za su yi amfani da shi.
Akwai likitoci da suka karanci abin da ya shafi fata, wanda komai ake buƙata a kan fata, idan an tuntuɓe su, za a dace.
Wasu mazan su ne ummul’aba’isin jefa mata a cikin harkar shafe-shafe a yau, amma da mata za su yi tunani a duk lokacin da suka faɗa matsala maza ƙalilan ne suke tsayawa don tausayawa mata yayin jinya. Don haka mata yana da kyau su yi wa kansu ƙiyamullaili don zama lafiya wadda Hausawa suke cewa, “ya fi zama ɗan Sarki.”
