Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
A yau idan ka zagaya makarantu a Nijeriya, daga garuruwa har ƙauyuka, za ka ga yara da manya suna koyon karatun boko — wanda ke nufin tsarin ilimin zamani da Turawa suka gabatar. Amma kafin wannan tsarin ya karɓu, akwai doguwar hanya da tarihi mai cike da abubuwan mamaki da al’adu daban-daban da suka taka rawa wajen samuwar karatun boko a Nijeriya.
Farkon zuwan Turawa da asalin karatun boko:
Karatun boko ya samo asali ne daga tsarin ilimi na Turawan mulkin mallaka, musamman na Birtaniya, waɗanda suka mamaye sassan Nijeriya tun ƙarshen ƙarni na 19. Kafin wannan lokaci, ilimi a Nijeriya yana ƙarƙashin makarantar allo, wato tsarin ilimin addinin Musulunci, musamman a Arewacin ƙasar, inda malamai ke koyar da Alƙur’ani da ilimin fikihu, nahawu da sauran fannonin addini.
A kudancin Nijeriya kuwa, kafin zuwan Turawa akwai tsarin koyon sana’o’i da ilimin gargajiya daga iyaye da dattawa. Amma zuwan mishanoni (missionaries) daga Turai, musamman daga ƙungiyoyi irin su Church Missionary Society (CMS), Roman Catholic Mission (RCM) da Wesleyan Mission, ya kawo sabon salo — ilimin da ake koyar da shi a cikin harshen Turanci.
Zuwan Mishanoni da fina makarantun farko:
An kafa makarantar farko ta boko a Nijeriya a shekara ta 1843 a Badagry, wacce mishanoni na CMS suka buɗe. A nan ne aka fara koyar da karatu da rubutu a Turanci, tare da darussa kamar lissafi, tarihi, da ilimin halin ɗan adam. A shekara ta 1859, aka fara buga jarida ta farko a Nijeriya mai suna Iwe Irohin a birnin Abeokuta — wannan ma ya zama wata kafa ta yaɗa ilimin boko.
Daga nan tsarin karatun boko ya fara yaɗuwa a yankin kudu, musamman a Legas, Kalaba, Onitsha da sauran birane. Amma a Arewa kuwa, karɓuwar wannan tsarin ta zo a hankali saboda dalilai da dama — musamman na addini da siyasa.
Dalilan da suka jinkirta karatun boko a Aaewacin Nijeriya:
Lokacin da Turawa suka mamaye Arewa a ƙarshen ƙarni na 19, sun tarar da tsarin ilimin Musulunci mai ƙarfi. Sarakunan Musulmi da malamai ba su ji daɗin zuwan karatun boko ba, domin sun ɗauke shi a matsayin hanya ta shigar da Kiristanci da lalata al’adunsu. Saboda haka, da farko, malamai da sarakuna sun nuna ƙin yarda da tsarin.
Sai dai gwamnatin mallaka ta Birtaniya ta yi amfani da dabarar haɗa karatun boko da tsarin mulkin mallaka. A shekara ta 1914, lokacin da Lord Lugard ya haɗa Arewa da Kudu, aka fara buɗe makarantun gwamnati a Arewa don horar da ‘yan aikin gwamnati, musamman masu fassara da masu rubuta takardu.
Faɗaɗa tsarin ilimi bayan mulkin mallaka:
Bayan samun ‘yancin kai a 1960, gwamnatin Nijeriya ta ɗauki ilimin boko a matsayin ginshiƙin ci gaban ƙasa. An kafa makarantun gwamnati a sassa daban-daban, kuma an fara buɗe jami’o’i kamar Uniɓersity of Ibadan (1948), Ahmadu Bello Uniɓersity, Zaria (1962), Uniɓersity of Nigeria, Nsukka (1960) da sauransu.
Tsarin karatu ya rabu zuwa matakai: Firamare, sakandare, da jami’a. Gwamnati ta kuma kafa hukumomi irin su Federal Ministry of Education da Nigerian Educational Research and Deɓelopment Council (NERDC) don kula da tsarin karatu da tsarin malamai.
Canje-canjen tsarin ilimi a lokutan daban-daban:
Tsakanin 1970 zuwa 1980, Nijeriya ta shaida babbar sauyi a tsarin karatu da aka kira Uniɓersal Primary Education (UPE), wanda aka ƙaddamar da shi a 1976 a zamanin Janar Olusegun Obasanjo. Wannan shiri ya buɗe ƙofofin makarantu ga miliyoyin yara, kodayake matsalolin kayan aiki da malamai sun kawo cikas.
Daga bisani, a 1999, gwamnatin Obasanjo ta sake gabatar da Uniɓersal Basic Education (UBE) don tabbatar da cewa kowane yaro ya samu aƙalla ilimi na asali kyauta.
Tasirin karatun boko a al’umma:
Zuwan karatun boko ya kawo babbar sauyi a rayuwar Nijeriya. Ya haifar da fitowar ‘yan siyasa, malamai, likitoci, injiniyoyi da manazarta da suka gina ƙasa. Ya kuma zama hanyar haɗin kai tsakanin Arewa da Kudu ta fannin sadarwa da ci gaban tattalin arziki.
Sai dai, akwai wasu ƙalubale da suka biyo baya — kamar yadda wasu ke ganin karatun boko ya rage darajar addini da al’adu, musamman a yankin Arewa. A wasu lokuta, matsalolin rashin aiki da cin hanci sun sa wasu suka ɗauki karatun boko da raina hankali.
Karatun boko a zamani na yanzu:
A yau, tsarin karatun boko a Nijeriya ya kai ga matakin zamani, inda ake haɗa shi da fasahar zamani (ICT). Ana koyar da kwamfuta tun daga makarantar firamare, sannan jami’o’i suna aiwatar da karatun nesa (online learning), musamman bayan ɓullar cutar COɓID-19.
Akwai kuma yunƙurin gwamnati da masu zaman kansu wajen inganta karatun sana’a da kimiyya (technical and ɓocational education), domin ba da damar aiki ga matasa.
Tarihin karatun boko a Nijeriya ya nuna cewa wannan tsarin ya samo asali ne daga zuwan Turawa, ya fuskanci ƙalubale na al’adu da addini, amma daga baya ya zama ginshiƙin ci gaban ƙasa. Duk da matsalolin da ake fuskanta — kamar rashin malamai, ƙarancin kayan aiki, da rashin daidaituwa tsakanin Arewa da Kudu — babu shakka karatun boko ya zama tushen ilimi da ci gaba a Nijeriya ta zamani.
