Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA
Haƙiƙa akwai jama’a da su ke zama lafiya a matsayin maguzawa a garuruwan Hausawa. Kama daga yankin Malumfashi a jihar Katsina, zuwa wajajen Sumaila a jihar Kano da ma yankunan jihar Jigawa har ma cikin ƙasar Gobir; a na samun maguzawa da ke zaune da iyalinsu lafiya kuma sun fi zama a ƙauyuka. A gefe guda yayin da maguzawa ke zama al’umma da ke rayuwa irin ta gargajiya da zabar rashin shin shiga Musulunci, akwai kuma wata ɗabi’a ta maguzanci da ba lallai sai a waɗannan yankuna da na lissafa ba. Za a iya samun maguzanci wato ɗabi’ar neman tada zaune tsaye a yankunan Arewa da su ka haɗa da Arewa ta tsakiya da cikin jihar Taraba da sauransu.
Na karanta a sassan iƙirarin da ‘yan kwangilar rusa Arewa ke yi cewa a baya a na ci mu su zarafi da cewa MAGUZAWA ne amma tun da hakan shi ne asalin Hausawa da ma Larabawa kafin zuwan musulunci to ai ba komai. Wasu ma kan ce a na amfani da kalmar don rage yawan Hausawa ne ko ma karya abun da su ke ayyanawa da gwagwarmaya duk da ma sakarci kawai su ke yi. A gaskiyar magana tun lokacin da Musulunci ya yi ƙarfi a arewacin arewa an raba jaki da duma an shata layi tsakanin Musulmi da maguzawa. Mun san cewa da ka ga Malam Bahaushe ka buga ma sa sallama don Musulmi ne. In ka ga wanda ba Musulmi ba a yankunan Hausawa ko na raba kan sa da Hausa to Bamaguje ne. A Kano akwai kwamitocin musuluntar da maguzawa. A na samun masu Musulunta a tsakanin maguzawa da kuma masu shiga addinin kirista sai waɗanda ke zama da addini ko ɗabi’un zamanin jahiliyya. An kawo labari mai inganci na taba samun wani Bamaguje ya yi shigar musulmi sak har a ka gabatar da shi ya jagoranci matafiya sallar azahar da la’asar don ya san tsarin don zama da Musulmi. Daga bisani ya tseguntawa daya daga matafiyan cewa shi ba Musulmi ba ne. Akwai ma cikin shahararrun littattafan Hausa inda a ka tambayi wani Bamaguje da gidansa ke makwabtaka da masallaci cewa shin ya san Allah? Nan take ya amsa da cewa “ga gida ga gida” wato ma’ana ai gidansa makwabcin gidan Allah ne!.
Duk magana da harshen Hausa da duk shigar burtu da wasu daga maguzawa da a ka ɗauka aikin makirci don sajewa da Musulmi, tsananin kiyayyarsu ga musulunci za ta bayyana don tabbas sai sun gaza jurewa shigar burtun su ayyana kan su da gidan da su ka fito. Shi ya sa da tunkuzar gyada ta ji matsa, sai wasu daga maguzawan da ke cikin ‘yan kwangila su ka fito fili a ka gane su, amma mafi taurin kai da makirci, ‘yan kwangila daga kananan ƙabilu kuma waɗanda ba Musulmi ba ke kara nitsewa a basaja. Ai ba mamaki don ɗan ƙullin mai abu in ya fi mai abu zafi.
A gurguje binciken da na ga an gudanar na asalin maguzawa ba zai wadatar da fahimta ba, fiye da su dai maguzawa mutane ne da su ka yi firr su ka ki shiga Musulunci kuma har ma sun fi son shiga kiristanci a wasu sassan don samun damar more rayuwar waman-taraka-baati-siddan-fa-huwa-finnaari. A tsarin mulkin Nijeriya kowa na da hurumin shiga addinin da ya kwanta ma sa a rai kuma ya yi bautarsa ba tare da tsangwama ba. Don haka haramun ne yin shigar burtu ga wani addini.
Na ga tarihi kama daga masu cewa maguzawa sun taso ne daga Habasha su ka taho Arewacin Nijeriya ta yau, ko kuma sun taho ne daga Afurka ta Arewa su ka iso Kano su ka saaje da Hausawa ko zama cikin ƙabilun da ke da’irar harshen Hausa. Maguzawan da su ka zauna a dutsen dala da ke cikin rukunin farko na mazauna Kano na addinin tsafi ne ƙarƙashin uwargijiya Tsunburbura da babban manzonsu Barbushe. Na ji da kunne na kwanaki a na hira da wani da ke ci gaba da bautawa Tsunburbura. Ga ma wasu iyayen gijin aljanunsu irin Giza-Gizai, Doguwa, Na’uwale mai ‘yan bori da sauran su shaidanu. Wayewa ta kawo mu dawowa daga rakiyar camfe-camfe da tsatsuba.
FASSARAR WANI ɗAN KWANGILA KAN MAGUZAWA
Wani ɗan kwangilar rusa Arewa da ke ayyana kan sa da Bamaguje ya ce don son zaman lafiyar maguzawa ne ya sa lokacin da Musulunci ya shigo ya yi ƙarfi sai kakanninsu su ka riƙa cewa “ba-ma-guje ba kuwa” ma’ana ba za su gudu ba kuwa don kar a tilasta mu su karɓar Musulunci. Daga waɗannan kalmomin a ka samu BAMAGUJE. Ba mamaki har zuwa yau a ke samun akasarin maguzawa a ƙauyuka da gudanar da sana’ar noma ta gado don ba dazukan farauta kuma akasarinsu ba su samu yin karatun boko ba don hakan haramun ne a gargajiyarsu ta maguzanci. Rashin ilimi na zamani balle addini kan bar mutane cikin duhun kai da kasa amincewa da sauran al’umma da su ka rabu da sabara. Abun da ya fito fili akwai cikin maguzawa da ba sa ƙaunar Musulunci sam-sam shi ya sa a ka samu wadanda ke hawa yanar gizo su ka karɓi kwangilar tada fitinar ƙabilanci a Arewa da duƙufa ga aibanta Shehu Mujaddadi da ya jagoranci hana kakanninsu tsafe-tsafe da shirka da rawar banjo, zunduma rawar mata mabiya ‘yan gurmi, su ’yar gagara, garaya da shan sautin molo a gidan shan barasa. Ba su tsaya nan ba su kan jinjinawa Chukwuma Nzegwu don shekar da jinin Firimiya Sir Ahmadu Bello da ya yi. Duk ayyukan alherin da Sardauna ya dasa a Arewa ababen kawar da ido ne a wajen su da nuna Sardauna bai yi komai ba na yabo.
Don haka in ka ga a ‘yan kwangila wani na haƙiƙancewa wajen zagin Shehu Mujaddadi da makircin cewa Fodiyanci sam…kaza da kaza to Bamaguje ne wato wanda ya tsere don kar ya yi Musulunci da zama ‘yan Musulunci haram. In abun zai tsaya ga kin shiga musulunci ai ba za a damu ba don kamar yanda na bayyana a baya tsarin mulkin Nijeriya ya ba wa kowa hurumin yin addinin da ya ga zai fishshe shi.
Akwai wasu Arewawa da su ka tsere kudu don gudun shiga Musulunci da a ka ba da labarinsu da zama ‘yan Gwandara, daga bisani sun karbi Musulunci amma harshensu ya karye su na surka Hausa da shagube ko cakudarsu da ƙabilun yankin Arewa ta tsakiya. An ruwaito cewa sun zabi RAWA da shiga musulunci sai a ke kiran su GWANDA mu su RAWA wajen more duniya da shagulgula maimakon shiga Musulunci mai ɗawainiyar yin sallah sau 5 a kullum. Ga azumi a watan Ramadan ga fidda zakka da hana holewa ta fitsara.
Wannan aikin da mu ke yi ya zama mai muhimmanci ne don ganar da musamman matasanmu kar su fada tarkon ‘yan kwangilar rusa Arewa. Hatta waɗanda su ka ba da kwangilar sai sun zabi wawayen mutane baubayin burmi ƙauyawan birni don yi mu su wannan mugun aiki. Duk wanda ka ga ya na wannan tafiya a kowane addini ya ke tantirin marar nazari ne don a karshe fitinar ai shi za ta fara cinyewa ko in shi ya na ƙetare wajen samun horo, iyayensa masu karamin karfi a ƙauyuka ne za su zama tokar farko. Mugayen mutane irin Ouba Ali Mohaman na Tibati na can wajen sayarwa Paul Biya makircin mara bayan Hausawa kamar yadda yaransa na nan Nijeriya ke yayatawa don ya samu muƙamin minista a gwamnati. In Allah ya yarda za a cafke shi don fuskantar hukuncin shirya ta’addanci kamar yadda ta faru ga ɗan uwansa Nnmadi Kanu. Kamaru ba za ta dauwama a mulkin Biya ba.
ƙananan alhaki ‘yan ku-cu-ku ba mu na ‘yan kwangila da ke nan Arewa na ganin ko ba a gane su ne. Haba ai duk bayanansu na nan a hannun jami’ai kuma tabbas za a cafke su a gabatar mu su da hujjoji kamar tsakiyar rana na haddasa fitina da su ke yi. Za ka samu mutumin da ba wanda ya san shi sai a soshiyal midiya amma za ka ga ya na tsilli-tsilli da ido wai shi dan gwagwarmaya ne. Gidan yari fa bai taɓa cika ba.
Ku biyo ni nan gaba da yardar Allah zan yi wa wasu tonon saala-saala.
KAMMALAWA
Ba mu da gida da mu ke tinƙaho da shi irin Arewa. Kama daga Sakkwato zuwa Yola, daga Ilori zuwa Maiduguri duk yankinmu ne mai faɗi da albarkar noma a kiwo ga tarin ma’adinai. Mu yi aiki tare don cin gajiyar arzikin da Allah ya horewa Lardin nan na Arewa. Ba za mu zuba ido wasu da ba su san darajar yankin ba su hada kai da maƙiya na ciki da wajen ƙasar nan wajen haddasa fitinar ƙabilanci. Ba wata riba a bar wasu su kawo fitina ta ƙabilanci, bambancin addini ko wani son zuciya. Tabbas magaba na Arewa sun yi iya bakin ƙoƙarinsu wajen aza Lardin kan turba mai kyau kafin su koma ga Allah. Uban kwarai Sir Ahmadu Bello ma sadaukar da ran sa ya yi karankataf don waɗanda za su zo a baya su amfana. Allah ya kiyeye garuruwanmu da ƙauyukanmu daga dukkan miyagun iri na fili da na ɓoye. Zama lafiya ya fi zama ɗan sarki.
