Shekarau ya yi tsokaci kan makomar siyasarsa, Tinubu, Atiku da Trump yayin cikarsa shekaru 70

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Tsohon Gwamnan Jihar Kano, Malam Ibrahim Shekarau ya ci alwashin cigaba da kasancewa ɗan siyasa har zuwa ƙarshen rayuwarsa, yana mai ikirarin shiga siyasa aiki ne da ya jiɓinci lamuran al’umma bisa jagorancin na gari a ƙasa.

Shekarau ya bayyana haka ne a ranar Laraba, yayin tattaunawa da manema labarai a gidansa da ke unguwar Munduɓawa a jihar Kano, yayin bikin cikarsa shekaru 70 a duniya inda ya yi tsokaci akan zangon siyasarsa, ƙalubalen da Nijeriya ke fuskanta da goben siyasar adawa yayin da ake tunkarar babban zaɓen 2027 a Nijeriya.

Tsohon Ministan na Ilimi ya ce ra’ayinsa na siyasa ya ginu ne akan hidimta wa ƙasa da al’umma bisa tsoron Allah, ba don wata manufa ta kai da kai ba.

“Zan cigaba da zama a fagen siyasa har ƙarshen rayuwata, kuma ba zan fita ba. Siyasa abu ne na hidimta wa al’umma, kuma muddin ina raye, zan cigaba da taka rawata”, inji shi.

Ya kuma kirayi ƴan Nijeriya da su riƙa shiga a dama da su a harkokin dimukraɗiyya domin tabbatar da samun jagorori na gari da za su ke yin shugabanci bisa gaskiya da adalci, yana mai cewa aikin siyasa wajibin addini ne akan ƴan ƙasa da suka san darajar kansu.

Ya tunatar da tarihin siyasarsa wanda ya samo asali tun a shekarun 1980s inda ya bayyana alfaharinsa na zama wanda ya doke gwamna mai ci a jiharsa ta Kano yayin zaɓen gwamna.

Ya bayyana cewa, jam’iyyar PDP duk da matsalolin rikicin cikin gida da take fama da shi, ita ce jam’iyyar adawa mafi nagarta, yana mai kira ga jam’iyyun ADC, LP da SDP da su haɗe da PDP domin karawa da mai mulki wato APC a manyan zaɓuka.

Da yake jawabi akan ayyukan gwamnatin Shugaba Bola Tinubu, Shekarau ya ce har yanzu tana aiki ne a matakin ƙasa da abinda ake buƙata musamman wajen yaƙi da ta’addanci inda ake cigaba da “yanka ƴan Nijeriya kamar dabbobi.”

Har’ilayau, ya yi gargaɗin shiga ƙamarin rikicin harkokin difulomasiyya tsakanin ƙasashen duniya yayin da Shugaba Donald Trump na Amurka ya ayyana Nijeriya a matsayin ƙasar da ake da damuwa akanta bisa zargin kisan kiyashi ga al’ummar Kiristanci, inda ya kuma yi ikirarin ɗaukar matakin soja akan Nijeriya matuƙar ba a daina ba.

By Babaji