
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Tsohon shugaban ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa na gwamnatin tsohon shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo, Manjo Janar Abdullahi Muhammed ya rasu.
An ruwaito cewa jami’in sojan mai ritaya ya rasu ne bayan shafe shekaru 86 a duniya a gidansa da ke Kaduna a safiyar ranar Laraba.
Marigayin, wanda aka fi sani da Adangba, ya taɓa zama gwamnan tsohuwar jihar Benuwai-Filato a zamanin soja daga 1975 zuwa Fabarairun 1976 lokacin mulkin Janar Murtala Muhammed.
Haka kuma a matsyinsa na haifaffen Ilorin a jihar Kwara, marigayin shi ne wanda ya samar da tsohuwar Ƙungiyar Tsaro ta ƙasa (NSO) wadda a yanzu aka sani da Hukumar ƴan sandan farin kaya (DSS) daga 1976 to 1979.
Sannan, ya riƙe muƙamin shugaban ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa a zamanin Shugaba Olusegun Obasanjo da Marigayi Umaru Musa Yar’Adua daga 1999 zuwa 2008.
Kazalika, shi ne Mai ba Shugaban Ƙasa Shawara akan Harkar Tsaro ga tsohon shugaban mulkin soji Janar Abdulsalami Abubakar (mai ritaya) daga 1998 zuwa 1999.
Har’ilayau, Kanal Abdul Muhammed kamar yadda aka san shi a shekarun baya, yana ɗaya daga cikin dakarun da suka kifar da gwamnatin Janar Yakubu Gowon a shekarar 1975.
