An samu Musulmi na farko a Amurka da ya zama magajin garin New York

Spread the love

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano

A karon farko a tarihin Amurka, Musulmi ya zama Shugaban Gwamnatin birnin New York (Mayor of New York). Mai suna Zohran Mahmood Mamdani, ɗan shekaru 34, wanda asalinsa daga ƙasar Uganda ne amma ya tashi kuma ya girma a Amurka.

Zohran ya shiga siyasa ƙarƙashin jam’iyyar Democrat, inda ya tsaya takarar shugabancin birnin New York, ya kuma kayar da ɗan takarar da shugaban ƙasa Donald Trump ya goyi baya.

Kazalika, rahotanni sun nuna cewa New York shi ne birni mafi girma da tasiri a Amurka, kuma yanzu Musulmi ne ke jan ragamar birnin — mai kula da kasafin kuɗi, tsaro, kiwon lafiya, sufuri da muhalli.

By ukarofi