Gwamna Raɗɗa ya sanya hannu kan aikin kwangilar samar da ruwan sha daga madatsar ruwa ta Zobe

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Wannan aiki kashi na biyu idan an kammala zai ba garuruwan Rimi, Charanchi,kafinsoli,Tafashya, Raɗɗa, karofi da Dutsinma wadataccen ruwan sha.

Haka kuma za a kafa bututun ruwan mai tsawon mita 88.74 da ƙarfafa cibiyar samar da ruwan sha na kafinsoli.

Idan an kammala aikin madatsar ruwan za ta samar da lita miliyan 1.5 na ruwan sha ga alummomin yakin da haɓaka noman rani ga ƙananan sana’o’i a yankin.

Gwamna Dikko Raɗɗa wanda ya ƙaddamar da aikin a garin kafinsoli ya ce yau shekara 47 da fara aikin gina Zobe Dam tun lokacin mulkin marigayi shugaban ƙasa Shehu Aliyu Shagari amma sai lokacin marigayi shugaban ƙasa Muhammadu Buhari aka buɗe madatsar ruwan.

“Yau gashi da yardar Allah zamu fara aiki kashi na biyu da zai taso daga madatsar ruwan zuwa wasu garuruwa na ƙananan hukumomi guda shida,”Inji gwamnan.

Gwamnan duk da bai fadi kuɗin da za a kashe wajen aikin ba,ya ce za a biya ɗan kwangilar kashi 40 bisa 100 na kuɗin aikin wanda ɗan kwangilar ya tabbatar wa gwamna Raɗɗa da kammala aikin cikin shekara ɗaya.

Malam Dikko Raɗɗa sai yayi kira ga hakimai da alummomin garuruwan da aikin ya shafa da su ba ma’aikatan haɗin kai domin gudanar da ingantaccen aiki da kuma ganin an kammala aikin akan lokaci.

By ukarofi