Harin Shanono: Ku dage da addu’o’in samun zaman lafiya – Sarkin Kano

Spread the love

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano

Mai martaba sarkin Kano Khalifa Muhammadu Sunusi na biyu, ya umarci hakimai da dagatai, da kuma masu unguwanni, da ma limaman masallatan Juma’a, da su ƙara dagewa da addu’o’n samun zaman lafiya a jihar Kano, da ma ƙasa baki ɗaya.

‎Sarkin ya bada wannan umarni ne a ranar Talata a bisa ganin yadda wasu mahara su ke shiga ƙaramar hukumar Shanono, inda kuma bisa yawan addu’ar har aka samu nasarar hallaka mutum 19 daga cikinsu.

‎Mai martaba sarkin ya kuma yabawa gwamnatin jihar Kano bisa tura jami’an sojoji, da jami’an tsaro na farin kaya akan lokaci, yana mai cewa addu’a kaɗai ce za ta kawo ƙarshen maharan.

‎Wakilin Blueprint Manhaja a Kano ya rawaito cewa, Mai martaba sarkin na kano Khalifa Muhammadu Sunusi II, ya kuma halarci taron buɗe sabon bankin Signature, da ke kan titin kasuwar Sabon Gari.

Yayin taron, wanda Gwamnan Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf ya jagoranci buɗewa, ya jaddada cewa buɗe irin wannan banki a Kano zai taimaka wajen samar da sabbin damarmakin kasuwanci, bunƙasa ƙananan masana’antu da kuma ƙarfafa tsarin hada-hadar kuɗi ta zamani.

By ukarofi