Daga RABIU SANUSI a Kano
Majalisar Zartarwar Jihar Kano, ƙarƙashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf, ta amince da kashe Naira biliyan 19.02 domin aiwatar da muhimman ayyuka a fannoni daban-daban na cigaban tattalin arziki da jin daɗin al’umma.
Kwamishinan yaɗa labarai da harkokin cikin gida na Jihar Kano, Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya ne ya bayyana haka yayin da yake ma Manema Labarai ƙarin haske bayan kammala zaman majalisar karo na 33 da aka gudanar a fadar gwamnatin Kano, ranar Asabar, 1 ga Nuwamba, 2025.
A cewar Waiya, majalisar ta tattauna muhimman batutuwa da suka shafi mulki, ci gaban tattalin arziki, da walwalar jama’a, inda aka amince da kashe ₦19,019,114,578.50 don aiwatar da ayyuka a fannoni guda shida da suka haɗa da ilimi, lafiya, ruwa, gine-gine, makamashi, da ofisoshin gwamnati.
A fannin ilimi, an ware ₦4.9 biliyan don biyan bashin abinci a makarantun kwana, gyaran makarantu da kuma tabbatar da samun kayan aiki a manyan makarantun gwamnati da jami’o’i.
A fannin lafiya, an ware ₦274 miliyan don gyaran Asibitin Tiga da Asibitin Hasiya Bayero na yara a cikin fadar Sarkin Kano.
Haka zalika, fannin ruwa ya samu ₦3.3 biliyan, wanda zai shafi samar da ruwan sha a wasu yankuna da kuma biyan wutar lantarki da mai na injinan tace ruwa.
Ma’aikatar Ayyuka da Gine-gine ce ta fi samun kaso, inda aka amince da ₦9.8 biliyan don gina sabbin hanyoyi, gyaran tituna, walda da hasken tituna, da kuma ayyukan kariyar ambaliya a cikin birnin Kano.
A ɓangaren makamashi da sabbin hanyoyin samar da wuta, an amince da ₦979 miliyan don samar da tsarin hasken rana (solar) a wuraren gwamnati, ciki har da Africa House da Sashen Harkokin Majalisar Gwamnati.
Majalisar ta kuma amince da gina gidaje 50 masu sauƙin farashi a kowace karamar hukuma a wajen birnin Kano, tare da siyan hannayen jari na KEDCO domin samar da wutar lantarki mai ɗorewa a jihar.
Waiya ya ƙara da cewa, majalisar ta amince da gabatar da manufar Wutar Lantarki ta Kano (Kano State Electricity Policy), domin tabbatar da tsari da ci gaba mai ɗorewa a harkar makamashi.
A yayin zaman, majalisar, ta kuma yaba da girmamawa da lambar yabo guda takwas da aka bai wa Gwamna Abba Kabir Yusuf daga cikin gida da ƙasashen waje bisa shugabanci na gari da jajircewa wajen kawo cigaba.
Daga cikin lambobin akwai Zartarwar Zinariya daga Jamhuriyar Guinea-Bissau, Zamka Award 2025, da kuma lambar yabo ta jaridar Independent a matsayin Jakadan Ilimi na Shekara.
A ƙarshe, majalisar ta tabbatar da ƙudirin gwamnati na ci gaba da yin aiki da gaskiya, bayyananniyar siyasa da himmar inganta rayuwar al’ummar Kano.
