Daga RABIU SANUSI a Kano
Tsohon Gwamnan Jihar Kano kuma jagoran jam’iyyar New Nigeria People’s Party (NNPP), Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya bayyana damuwa kan matakin Shugaban ƙasar Amurka, Donald Trump, bayan da ya ayyana Najeriya a matsayin “ƙasa mai matsala ta musamman” (country of particular concern).
Kwankwaso ya bayyana haka ne cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Facebook a ranar Lahadi, inda ya ce kalaman Trump abin damuwa ne, tare da kira ga gwamnatin Amurka da ta rungumi hanyar haɗin kai da taimako maimakon fitar da kalamai da za su raba kawunan ‘yan Najeriya.
“Abin da ya kamata a fahimta shi ne, ƙasarmu ƙasa ce mai cikakken ‘yanci, wacce jama’arta ke fuskantar barazana daga miyagu a sassa daban-daban.
Matsalar tsaro da muke fama da ita ba ta bambanta tsakanin addini, ƙabila, ko ra’ayin siyasa,” in ji Kwankwaso.
Ya Kuma bayyana cewa maimakon yin hukunci ko tsokaci da ka iya haifar da rarrabuwar kawuna, ya fi dacewa Amurka ta tallafa wa Najeriya da fasahohi na zamani domin taimakawa hukumomin tsaro wajen yaƙi da miyagun laifuka.
“Ya kamata Amurka ta taimaka wa hukumomin tsaro na Najeriya da kayan aiki na zamani domin magance matsalar tsaro, ba wai ta yi kalamai da za su ƙara raba kan ‘yan ƙasa ba,” in ji shi.
Kwankwaso ya kuma shawarci gwamnatin tarayya da ta kafa jakadu na musamman daga cikin gogaggun ‘yan diflomasiyya domin tattaunawa da gwamnatin Amurka, tare da tabbatar da cewa an naɗa jakadu na dindindin da za su kare muradun Najeriya a ƙasashen waje.
Haka kuma, ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su tsaya tsayin daka wajen kare martabar ƙasa da kuma ƙarfafa haɗin kai a tsakanin al’umma.
“Ya ‘yan uwana ‘yan ƙasa, wannan lokaci ne da ya dace mu fifita haɗin kai da zumunci fiye da rarrabuwa.
