Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Sakataren Majalisar ɗinkin Duniya (MDD), Antonio Guterres, ya bayyana cewa lokaci ya yi da za a yi gyaran fuska a manyan majalisun duniya, musamman Majalisar Tsaro ta Majalisar ɗinkin Duniya, domin su dace da yanayin siyasa da tattalin arzikin duniya na yanzu.
Yayin wata tattaunawa ta musamman da aka shirya a ranar Litinin don tunawa da cika shekaru 80 da kafa Majalisar ɗinkin Duniya, Guterres ya bayyana rashin samun kowace ƙasa ta Afirka a matsayin memba mai kujerar dindindin a Majalisar Tsaro a matsayin abin kunya da ke buƙatar gaggawar gyara.
Ya ce, tun bayan kafuwar MDD shekaru takwas da suka gabata, ƙungiyar ta taka rawar gani wajen hana barkewar yaƙin duniya na uku, da warware rikice-rikicen da suka addabi duniya, tare da cimma manyan nasarori da ba a taɓa zato ba a shekarar 1945.
“Majalisar ɗinkin Duniya yanzu tana taimaka wa mutane sama da miliyan 150 a kowace shekara da abinci da agajin jinƙai, sannan tana ba da rigakafi ga kusan rabin yaran duniya,” inji shi.
Ya ƙara da cewa, MDD tana tallafa wa gudanar da zaɓe a ƙasashe da dama, tana kuma tsare doka da tsarin duniya ta hanyar yarjejeniyoyi da fiye da 80 da suka shafi kare muhalli, ‘yancin ɗan adam da ‘yancin faɗar albarkacin baki.
Guterres ya ce, ƙungiyar ta taka muhimmiyar rawa wajen aiwatar da shirye-shiryen agaji a duniya, taimakawa ‘yantar da ƙasashe sama da 80 daga mulkin mallaka, gyaran barnar da aka yi wa sararin samaniya (ozone layer), da kuma ƙarfafa Yarjejeniyar ƙasa da ƙasa kan Haƙƙin ɗan Adam.
Ya bayyana tarihin MDD a cikin shekaru 80 a matsayin shaida cewa haɗin kai da fahimtar juna na iya rinjayar duhun rikice-rikice da rashin adalci.
Sai dai ya ce yanzu duniya ta shiga sabon zamani na kalubale mai tsanani — inda sararin dimokuraɗiyya ke ƙara raguwa, rikice-rikice ke ƙaruwa, da kuma matsalar sauyin yanayi ke ta’azzara.
