Daga DAUDA USMAN a Legas
Shugaban sashen kasuwancin dankalin turawa na kasuwar Mile 12 International Market da ke Legas, Alhaji Bala Magaji Gozaki, ya bayyana cewa kasuwar Mile 12 ta zama babbar kasuwa a Nijeriya da ma Afrika baki ɗaya, bisa yawan al’ummar ƙasashen waje da ke gudanar da cinikayya a cikinta.
Alhaji Bala Magaji, wanda asalinsa daga karamar hukumar Kafur ta jihar Katsina ne, ya ce kasuwar ta kai matsayin da za a iya cewa “kasuwa ta ƙasa da ƙasa” saboda irin ci gaba da haɓakar da take samu a kowanne bangare, musamman wajen jawo ‘yan kasuwa daga ƙasashen makwabta.
Ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da Blueprint Manhaja a Legas, inda ya ce, “A yau kasuwar Mile 12 Intanashanal Maket ta zarce yawancin kasuwannin da ke ƙasashen Afrika, tunda a kullum ana samun sababbin ‘yan kasuwa daga waje da suke zuwa domin hada-hadar kayan amfanin gona.”
Alhaji Bala Magaji ya jinjinawa shugabancin kasuwar ƙarƙashin Alhaji Shehu Usman Jibrin Samfam, wanda ya ce matashi ne mai hangen nesa, ilimi da ƙwarewa, wanda jagorancinsa ya ƙara tabbatar da cigaba da daidaiton kasuwar.
A cewarsa, “Shehu Samfam shugaba ne mai jajircewa, wanda Allah Ya azurta da hikima da dabarar tafiyar da al’amuran kasuwa. Jagorancinsa ne ya sa yanzu kasuwar ke ci gaba cikin lumana da bunƙasa ta kowanne ɓangare.”
Ya kuma buƙaci shugabannin sassa da dukkan ‘yan kasuwa masu gudanar da sana’o’i daban-daban a cikin kasuwar da su ci gaba da bai wa shugabancin kasuwar hadin kai da goyon baya domin tabbatar da nasarar ci gaban kasuwancin gaba ɗaya.
Haka kuma, Alhaji Bala Magaji ya yi kira ga ‘yan kasuwa da su kula da rijistar katin zabe nasu yayin da ake cikin yanayin siyasa, inda ya ce wasu katunan sun lalace ko kuma sun ɓace, don haka akwai buƙatar su je cibiyoyin gyara domin sabunta su.
A ƙarshe, shugaban sashen kasuwancin dankalin turawa na Mile 12, Alhaji Bala Magaji Gozaki, ya yi addu’a ga Nijeriya, yana fatan Allah Ya ci gaba da zaunar da ƙasar lafiya tare da bunƙasa arzikin al’umma baki ɗaya.
