Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Hukumar Jarabawa ta ƙasa, NECO, ta buɗe cibiyar zana Jarabawar Kammala Makarantar Sakandare (SSCE) a birnin London, da ke ƙasar Biritaniya.
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mukaddashin Daraktan Yada labarai da Hulɗa da Jama’a na hukumar, Azeez Sani, ya fitar a ranar Lahadi a Abuja.
Sani ya ce wannan shiri na da nufin samar da damar yin jarabawa mai inganci da sauƙi ga ‘yan Nijeriya da ke zaune ƙasashen waje, musamman waɗanda ba su samu damar kammala karatun sakandare ba ko kuma samun takardar da ta yi daidai da hakan.
Ya ambaci Shugaban Hukumar NECO, Farfesa Dantani Wushishi, wanda ya ƙaddamar da cibiyar yayin wani taro kan ilimi a London na cewa an ɗauki wannan mataki ne domin wayar da kan masu ruwa da tsaki game da kasancewar NECO a ƙasar Biritaniya.
Farfesa Wushishi ya ce an kafa wannan sabuwar cibiyar ne tare da haɗin gwiwar Barnfield Education Ltd., London.
