09
Dec
Daga BAKURA K. MUHAMMAD a Bauchi Sabon kwamishinan ‘yan sanda da aka tura jihar Bauchi, Umar Mamman Sanda, ya sha alwashin jajircewa wajen murƙushe duk watni ƙalubale da kan taso a jihar bisa manufofin Babban Sufeton ‘yan sanda na ƙasa, Alkali Baba Usman da Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari. Sai dai, sabon kwamishinan ya bayyana cewar, za a samu biyan wannan buƙata ce kaɗai idan an ƙwamatsi haɗin kan sauran hukumomin tsaro da ke cikin jihar, don haka ya sha ɗamarar haɗin kai da su domin tabbatar da ingantuwar rayuwar ɗaukacin jama’ar jihar. Sabon kwamishinan ‘yan sandan yana yin jawabi ne…
