Ana kai ruwa rana kan shugabancin siyasar ’yan Arewa a Legas

Daga JAMIL GULMA a Legas

A duk lokacin da mutane biyu ko fiye ke neman abu ɗaya kuma ko ta halin ƙaƙa su na ganin sai haƙarsu ta cimma ruwa dangane da samun abinda su ke so, to ba shakka akwai gumurzu.

Yanzu haka dai iskar guguwar siyasa ta soma kaɗawa a faɗin Nijeriya, inda masu neman wakilci da kuma shugabanci a matakai daban-daban na siyasa sai kai-komo suke yi, don ganin sun sami cimma muradinsu.

Jihar Legas ma ba a bar ta a baya ba, sai dai a jihar abinda ya fi ɗaukar hankali, musamman a ɓangaren ’yan Arewa, bai wuce wane ne zai jagoranci siyasar jihar ba ta yadda za su sami romon dimukraɗiyya da zai kai kowane saƙo da lungu, musamman a ɓangaren ’yan Arewa mazauna Legas.

Tun lokacin da aka ayyana Alhaji Sa’adu Yusuf Dandare Gulma a matsayin shugaban Jam’iyyar APC Arewa a jihar ta Legas, sai cikin waɗansu ya ɗuri ruwa, musamman waɗanda ke rawa da bazar ’yan Arewa a cikin gwamnatin jihar.

Wakilin Manhaja ya zanta da ɗaya daga cikin jagororin siyasar Legas a ƙarƙashin jam’iyyar ta APC kuma wanda yana daga cikin mutanen da suka yi uwa da makarɓiya wajen ganin samun nasarar jam’iyyar, amma kuma sai bayan an ci yaƙi aka bar su da kuturun bawa.

Sai dai Hausawa su kan ce, waiwaye adon tafiya. Tarihin siyasar Jihar Legas ba zai cika ba ba tare da la’akari da irin gudunmawar da ’yan Arewa suke bayarwa ba, haka-zalika tarihin ’yan Arewa a Legas ba zai kammala ba ba tare da sanin yadda ya shigo ba.

Waxansu bayanai da Wakilin Manhaja ya tattara sun bayyana cewa, ɗan Arewa ya zo Legas tun ƙarni na 17 kafin zuwan Turawan Mulkin Mallaka kuma da sana’arsa ya ke tun a wancan lokacin.

Tun a wannan lokacin Bahaushe yana zaune a waɗansu wurare daban-daban a Kudancin ƙasar, amma sai dai Agege nan ne babban zango, inda bayan an sauka daga nan masu tafiya wasu sassan kudanci da suka haɗa da Ibadan da Shagamu da Abeokuta Ijebu da sauransu haka zalika da kuma wajen ƙasar da suka haɗa Ghana da Togo, Borkina Faso, Dahomey (Benin a yanzu) da dai sauransu. Haka zalika, idan fatake, musamman na goro suka shigo daga Ƙasar Ghana, Agege ne babban zango, inda a nan ne ake yin hada-hadar kasuwanci. 

Bayan samun ’yancin kai a shekarar 1960 a Jamhuriya ta ɗaya Hausawa sun tsunduma fagen siyasa a kudancin ƙasar, musamman a cikin jam’iyyar Action Group (AG) yayin da a Jamhuriya ta Biyu, wato zamanin Alhaji Shehu Shagari, har waɗansu ’yan Arewa sun sami gurabe a qananan hukumomi. Haka nan har zamanin SDP da NRC.

Bayan dawowa mulkin dimukraɗiyya a shekarar 1999, Alhaji Idi Mai Kapet ya zama shugaban jam’iyya a ɓangaren ’yan Arewa na farko zuwa Alhaji Ganiyu Abdulgaffar har zuwa Alhaji Ibrahim Sidi Ali (Allah Ya jiƙan su). Bayan rasuwar Sidi Ali Said, mataimakinsa Alhaji Muhammadu Dandamma Yabo, ya ɗare kujerar, inda ya zamo shugaba a jam’iyyar Action Congress of Nigeria (ACN).

Sai dai duk da irin rawar da ’yan Arewa ke takawa a fagen siyasar Legas, ba su sami wani romon siyasar ba tun kama daga ’yan siyasar zuwa sarakunan gargajiya da ’yan kasuwa. Wannan rashin samun romon dimukraɗiyyar ne ya fargar da su daga barcin da suke, inda suka ga babu mafita wacce ta wuce su haɗa kai waje ɗaya su yi magana da murya ɗaya, wanda shi ne ake a kai yanzu.

Alhaji Maikudi Haruna (Baba Etoo), wani ɗan kasuwa kuma ɗan siyasa, ya bayyana wa Wakilin Manhaja cewa, a siyasar Jihar Legas, idan ka cire Yarabawa, to babu wata al’umma da ta ke bayar da irin gudunmawa da ta ke bayarwa kamar Hausawa, saboda yanzu haka akwai ’yan Arewa sama da milliyan biyar da sun zama ’yan Legas, saboda a nan aka haifi iyayen waɗansu ma, wasu kuma a nan aka haife su. Saboda haka ba su da wani garin da suke alfahari da shi da wuce Legas, amma sai dai yawan da gudunmawar da su ke bayarwa yana neman zama aikin banza, saboda har yanzu ba wata al’ummar Arewa da za ta bugi ƙirji ta yi alfahari da wani abu na cigaba da ta samu a siyasance.

Alhaji Haruna ya ƙara da cewa, yanzu haka mutumin da ke rawa da bazar ’yan Arewa da ke riƙe da muƙamin Kwamishina a Ma’aikatar Tsare-tsaren Gine-ginen Bakin Ruwa da sunan ’yan Arewa, Hon. Kabiru Ahmed Abdullahi, yana kallon kowa jahili ne. Saboda haka ba ya kowacce irin hulɗa da kowa ballantana al’umma su sami kafar aikawa ko samun wani saƙo tsakaninsu da Gwamnatin Jihar Legas, wanda yana daga abubuwan da suka fargar da ’yan Arewa har suke ganin da ya ke yanzu an sami sabon salon shugabanci in sha Allahu haƙar ’yan Arewa za ta cimma ruwa, saboda kowa zai shigo a tafi tare inda kowane mutum zai sami damar bayar da ta sa gudunmawa kuma ba zancen waɗansu ’yan tsirarrun mutane su ware kan su suna yin yadda suka ga dama. Siyasa ta al’umma ce, saboda haka za a kasa ta a faifai.

Wakilinmu ya nemi jin ta bakin Alhaji Kabiru Ahmed Abdullahi, don jin ta bakinsa, sai dai hakan ba ta samu ba, saboda a duk lokacin da ya kira shi, wayar ta kan ce ba ya kusa, inda daga ƙarshe ya tura masa saƙon kar-ta-kwana, amma dai har zuwa lokacin haɗa wannan rahoton babu amsa.

Yanzu haka dai an ja daga tsakanin ɓangarorin siyasar guda biyu, waɗanda ba sa ga maciji a siyasance, inda ɓangaren Alhaji Kabiru Abdullahi, wanda ya ke riƙe da muƙamin Kwamishina da sunan ’yan Arewa da kuma sabon shugaban Jam’iyyar APC Arewa Community Reshen Jihar Legas, Alhaji Dandare Gulma, wanda ake ganin ya na da goyon bayan sarakuna da ’yan kasuwa da ƙungiyoyin matasa na siyasa da na sa-kai da kuma ’yan siyasar da a ke hasashen yana da kashi 95 na goyon bayan ’yan Arewa da ke Jihar Legas.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *