Sabon kwamishinan ‘yan sandan Bauchi ya sha alwashin yin aiki bisa tsarin doka

Daga BAKURA K. MUHAMMAD a Bauchi

Sabon kwamishinan ‘yan sanda da aka tura jihar Bauchi, Umar Mamman Sanda, ya sha alwashin jajircewa wajen murƙushe duk watni ƙalubale da kan taso a jihar bisa manufofin Babban Sufeton ‘yan sanda na ƙasa, Alkali Baba Usman da Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari.

Sai dai, sabon kwamishinan ya bayyana cewar, za a samu biyan wannan buƙata ce kaɗai idan an ƙwamatsi haɗin kan sauran hukumomin tsaro da ke cikin jihar, don haka ya sha ɗamarar haɗin kai da su domin tabbatar da ingantuwar rayuwar ɗaukacin jama’ar jihar.

Sabon kwamishinan ‘yan sandan yana yin jawabi ne yayin farkon ganawar sa da manema labarai jim kaɗan bayan ya kama aiki a Bauchi a ranar Litinin tamakon jiya, inda yake cewa, manufar tsarin zamani na kula da rayuka da dukiyoyi haɗi da hana aikata miyagun laifuka, kamar yadda ake gudanarwa a wannan duniya tamu, sun rataya ne bisa yarda da amincewa da juna a tsakanin jama’a.

Ya ce, “waɗannan ɗabi’u da manufofi sune jigon jajircewar mu, a ɗaiɗaiku ko jimlace wajen nusar da bin dokoki da umarni a ɗaukacin faɗin jihar Bauchi. Za mu tabbatar da cewar, an kakkaɓe miyagun laifuka a tsakanin jama’a bisa bin hanyoyin dokoki, ƙa’idoji da mazowa umarce-umarcen hukumomi.

Sanda ya bayyana cewar, jami’an rundunar ta Bauchi za su gudanar da ayyukan su ne bisa ƙwarewa kan akalar ilimin yaƙi a zangonnin fasaha daban-daban, domin tsarin gudanar da ayyuka bisa azama, kariya, har da mayar da martani.

Kamar yadda kwamishina ya ce, waɗannan halaye za a wanzar da su ne da himmatuwar jama’a, gamayyar su, da jajircewar su, faragar warware matsaloli da gudummawar al’umma domin tabbatar da zaman lafiyar jama’a.

“Dabarbarun mu na gudanar da ayyuka za su dogara ne kan ilimin tafiyar da tsaron jama’a bisa tafarkin bin dokoki da ka’idojin zamantakewa domin cimma buqatar tsaro ta hanyar ƙwarewa haɗi da gudummawar jama’a.”

Ya kuma bayar da tabbacin cewar, rundunar ‘yan sanda ta jihar Bauchi ƙarƙashin jagorancin sa za ta yi aiki da ƙa’idojin fasahar zamani kan tsaro domin bibiyar masu laifuka a dabobi da maɓoyar miyagu da wuraren tarurrukan jama’a da zummar tabbatar da tsaro a cikin al’umma.

Sanda ya ce, “sadaukar da kai na ga tsaron jama’a shine babban manufar aiki na, tsare rayuka da dukoyoyin jama’a, kare maras laifi daga yaudara, maras ƙarfi daga mai kama-karya, da tabbatar da zaman lafiya tsakanin jama’a, tare da yin hani ga tashin-tashina da ƙetare iyaka.”

Ya yi matuƙar yaba wa babban Sufeton ‘yan sanda na ƙasa, Alkali Baba Usman bisa damar da ya ba shi na gudanar da ayyukan cigaban ƙasa, ya kuma nemi haɗin kai da goyon bayan masu ruwa da tsaki, da ɗaukacin jama’a baki ɗaya wajen gudanar da ayyukan sa na tsaro da wanzar da zaman lafiya.

Malam Umar Mamman Sanda dai, kafin turo shi Bauchi a matsayin kwamishinan ‘yan sanda na 43 a jihar, shi ne kwamishina mai kula da dakaru a fannin binciken sirri na helkwatar tsaro da ke birnin Abuja.

Kwamishinan ‘yan sanda mai barin gado a Bauchi, Abiodun Sylvester Alabi wanda yanzu ya koma fannin da magajin sa ya taso a Abuja, a cikin jawabin bankwana, ya gode wa Babban Sufeton ‘yan sanda na ƙasa, Alkali Baba Usman bisa damar da ya ba shi na kasancewa kwamishinan ‘yan sanda a jihar Bauchi.

Alibi ya bayyana cewar, a lokacin gudanar da ayyukan sa a matsayin kwamishinan ‘yan sanda na 42 a jihar Bauchi, jami’an rundunar sa sun yi matuqar iyakar iyawa wajen kare rayuka da dukiyoyin jama’a, haɗi da tabbatar da zaman lafiyar al’umma.

Mista Abiodun Alabi ya jinjina wa haɗin kai, goyon baya da fahimtar juna da ke tsakanin rundunar sa da ɗaukacin jama’ar jihar Bauchi waɗanda suka zama na cimma nasarorin da ya samu a cikin watanni tara na kasancewar sa kwamishinan ‘yan sanda.

Ya yaba wa shugabannin hukumomin tsaro mazauna cikin jihar, sarakunan gargajiya da shugabannin addinai, kwamitin hulɗa tsakanin ‘yan sanda da jama’ar gari, haɗi da kafofin watsa labarai waɗanda ke wayar da kan jama’a kan gujewa aikata miyagun laifuka ko shiga sharo ba shanu.