Da ɗumi-ɗumi: ’yan bindiga sun sake kai hari masallaci a Neja, sun halaka mutum 15

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Aƙalla masallata 15 ne suka mutu yayin da wasu da dama suka samu rauni a harin da aka kai a masallaci da ke ƙauyen Ba’are a ƙaramar hukumar Mashegu na jihar Neja.

Maharan sun kai harin ne yayin da mutanen ƙauyen ke sallar asubahi kamar.

Wata majiya ta ce, an garzaya da waɗanda suka jikkata zuwa babban asibitin Kontagora domin yi musu magani.

Kwamishinan ’yan sandan jihar Neja, Monday Bala Kuryas, ya tabbatar da harin, ya ce, aƙalla mutane 9 aka kashe a harin.

Ya jadada cewa, hukumomin tsaro za su cigaba da yin ayyukansu na kiyaye rayuka da dukiyoyin ’yan jihar Neja da ‘yan Nijeriya yayin da ya ke kira ga al’umma su riƙa taimaka musu da bayanai masu amfani.

Wannan harin na zuwa ne kimanin watanni biyu bayan ‘yan bindiga sun halaka mutane 18 a wani masallaci a ƙaramar hukumar ta Mashegu.

An kai wancan harin ne a ƙauyen Mazakuka da ke ƙaramar hukumar Mashegu a ranar 26 ga watan Oktoba.