Kamfanin Dangote ya ƙaddamar da horon ‘yan jarida 60 a Arewa maso Yamma

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

A ranar Larabar makon jiya Kamfanin Ɗangote ya ƙaddamar da wani shiri na horas da ‘yan jarida 60 daga jihohin arewa maso yamma a jihar Kano.

A cewar fannin hulɗar jama’a na kamfanin, horon wani ɓangare ne na tsarin ayyukan sauke nauyin al’umma da kamfanin ke yi.

Horon, a cewar kamfanin, an yi shi ne da nufin ƙara ƙaimi kan fasahar kafafen yaɗa labarai, wanda aka gayyato ‘yan jarida daga jihohin Sakkwato, Katsina, Kebbi, Kano, Kaduna, da kuma Jigawa.

Horon na haɗin gwiwa ne da Kamfanin Folio Media and Creative Academy, inda kamfanin ya ce an gudanar da shi a baya a wasu shiyyoyin ƙasar.

Taron na kwanaki uku an yi masa take da “Haɗewar aikin jarida ta hanyar fasaha.”

A taron da aka fara gudanar da horon a Kano ranar Laraba, shugaban rukunin kamfanin, Branding and Communication, Anthony Chiejina, ya ce an shirya horon ne domin inganta ƙwazon ‘yan jarida kan dabarun yaɗa labarai.

Ya ce horon zai taimaka wajen samar wa manema labarai damar tunkarar ƙalubalen da ke tattare da sauya salo daga gargajiya zuwa sabbin dabarun yaxa labarai.

Ya bayyana cewa akwai alaƙa mai kyau tsakanin kamfanin da kafafen yaɗa Labarai.

Mai kula da wannan shiri a Folio Media and Creative Academy, Alabi Pius, ya ce cibiyar (FMCA) ita ce ta horar da Folio Communications Plc.

Mawallafin na jaridar Daily Times, ya ƙara da cewa an shirya wannan horon ne domin bai wa ‘yan jarida da shugabannin kafafen yaɗa labarai da jami’an hulɗa da jama’a da ma na wasu fannoni daban.

A nasa jawabin, wani malami a Jami’ar Bayero Kano, Dr. Mukhtari Magaji, ya buƙaci ‘yan jarida da su yi shirin sauyawa zuwa zamani, domin fasahar za ta ƙara musu ƙarfin gwiwa da kuma sanya su cikin sabuwar duniya.

Dokta Magaji ya bayyana cewa haɗa aikin yaɗa labarai na nufin amfani da rubutu, sauti, da bidiyo ta hanyar sadarwa guda ɗaya.

Sauran malaman da za su yi jawabi a shirin horaswar sun hada da Dr. Bala Muhammad, tsohon ɗan jarida a kafar yaɗa labarai ta BBC da ke Landan kuma malami a Jami’ar Bayero Kano; da kuma Dr. Saminu Umar, shi ma malami a wannan jami’ar.

A nasa jawabin, wani da ya halarci taron kuma wanda ya samar da shafin intanet na “Good Governance”, Dakta Aliyu Machika, ya ce horon ya yi daidai da lokaci domin zai bai wa manema labarai a shiyyar Arewa maso Yamma damar ƙara ƙaimi da kuma ƙara musu ƙarfin tattalin arziki.