Yadda kwantena ta rikito kan uwa da yaranta 3 a Kwara

Daga BASHIR ISAH

A ranar Talatar da ta gabata aka samu aukuwar wani mummunan haɗari a Ilorin, jihar Kwara inda sunduƙin ɗaukar kaya da aka fi sani da kwantena, ya rikito daga saman tirelar da ke ɗauke da shi ya faɗa kan wata mata da ‘ya’yanta su uku sa’ilin da suke cikin mota.

An yi zargin cewa haɗarin ya auku ne sakamakon ƙoƙarin tserewa da direban motar da ke ɗauke da sunduƙin ya yi bayan da jami’an yaƙi da fasa-ƙwauri suka tasa shi gaba.

Binciken MANHAJA ya gano cewa wannan na zuwa ne kimanin wata guda da faruwar wata arangama a yankin tsakanin matasa da jami’an Kwastam sakamakon yinƙurin cafke wani direban tirela da aka yi bisa zargin yana ɗauke da haramtattun kayayyaki.

Haka nan, faruwar haɗarin ya haifar da tsaiko ga zirga-zirgar abubuwan hawa a yankin na tsawon lokaci.

Kwantenar ta faɗo kan wata ƙaramar mota ce wadda wata mata da ‘ya’yanta uku ke ciki. Duk da dai babu hasarar rai a haɗarin, amma dai matar wadda ita ce ke tuƙa motar, tare da ɗaya daga cikin yaran sun ji rauni.

An kwashi waɗanda haɗarin ya rutsa da su zuwa asibitin da ke kusa bayan da aka samu nasarar zaƙulo su, inda yanzu haka suke ci gaba da samun kulawar likitoci.

Bayanai sun tabbatar da cewa fafarar da jami’an Kwastam suka yi wa motar bisa zargin tana ɗauke da shinkafar ƙetare da aka hana shigowa da ita cikin ƙasa, hakan ne ya yi sanadiyar aukuwar haɗarin.

Sai dai jaridar Daily Trust ta rawaito cewa, Mai magana da yawun Hukumar Kwastam na Kwara, Chado Zakari, ya musanta fafarar da aka ce jami’ansu sun yi wa babbar motar.