Jami’an Kwastam sun kama tsabar kuɗi Naira miliyan 71.350 da wasu haramtattun kayayyaki a Katsina

Daga UMAR GARBA a Katsina

Hukumar Kwastam reshen jihar Katsina ta kama maƙudan kuɗaɗe har Naira miliyan 71.350 da aka ɓoye cikin jakar ‘Ghana Must Go’.

Muƙaddashin shugaban hukumar a Katsina Ɗalha Wada Chedi ne ya bayyana haka a wani taron manema labarai da hukumar ta kira a birnin Katsina.

Wada Chedi ya ƙara da cewa an kama waɗannan tsabar kuɗaɗe ne a kan iyakar Jibiya da ke jihar Katsina.

“Mun kama tsabar kuɗi har Naira miliyan 71.350 waɗanda aka ɓoye cikin jakar ‘Ghana Must Go’ a iyakar Jibiya cikin wata mota ƙirar Toyota, wadda wasu mutane uku ke tuƙawa, mun kama mutanen, mun kuma kai kuɗin ajiya a Babban Bankin Nijeriya reshen jihar Katsina.”

Ya ƙara da cewa hukumar ta yi nasarar kama wasu muggan wuƙaƙe da ake kira Jack Knife a turance waɗanda adadin su ya kai guda 186, inda kuɗinsu ya kai Naira 542,900 an kama wuƙaƙen a hanyar Jibiya zuwa Batsari ɗaya daga cikin hanyoyin da ke fuskantar ta’addancin ‘yan bindiga.

Shugaban hukumar ya ci gaba da cewa “sauran haramtattun kayan da muka kama sun haɗa da muggan wuƙaƙe guda 186 waɗanda kuɗinsu ya kai Naira 542,900, mun kuma kama motoci ƙira daban-daban guda takwas, mun kuma kama buhunan shinkafar ƙasar waje guda 281, sai kuma ƙaton ɗin taliya guda 498 da kuma buhunan madara na ƙasar waje guda bakwai.

“Mun kuma kama jarkokin man girki na ƙasar waje guda guda 22, mun kuma kama ƙaton goma na maganin Diclofenac, sai buhunan kanwa guda 3, katan na madara guda 35, da buhunan man fetur guda 75, sai kuma ɗaurin kayan gwanjo guda 37,” inji shi.

Chedi ya bayyana cewar adadin harajin kayan da hukumar ta kama ya kai Naira miliyan 176,453,850.