Sojoji sun ceto ‘yan sanda 20 daga hannun ISWAP

Daga BASHIR ISAH

Biyo bayan martanin da sojojin Nijeriya suka mayar kan harin da mayaƙan Boko Haram/ISWAP suka kai ofishin ‘yan sanda na Buni Yadi a jihar Yobe a Juma’ar da ta gabata, hakan ya sanya jami’an tsaron suka samu nasarar ƙwato duka ‘yan sanda su 20 da ‘yan ta’addar suka yi garkuwa da su yayin harin nasu.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da jami’an tsaro suka yi nasarar halaka mutum 91 tsakanin ‘yan fashin daji da ‘yan bindiga da masu garkuwa da mutane a yankunan Kala Balge, Rann, Dikwa da kuma Biu a jihar Borno, da Gombi a jihar Adamawa haɗa da jihar Zamfara.

Muƙaddashin Darakta Sashen Yaɗa Labarai na Rundunar Sojojin Nijeriya, Brig-Gen Bernard Onyeuko, shi ne ya bayyana haka a Abuja. Yana mai cewa, duk da nasarorin da suka samu, su ma sun rasa wasu dakaru yayin arangamarsu da ‘yan ta’addan a lokuta mabambanta.

Da yake ƙarin haske kan ayyukan sojojin game da yaƙi da ayyukan ɓata-gari, Onyeuko ya ce sojoji sun daƙile harin Boko Haram/ISWAP a ranar 3 ga Disamban 2021, lamarin dabya haifar da musayar wuta tsakanin ɓangarorin biyu a yankin ƙaramar hukumar Kala Balge a jihar Borno, inda a nan ma suka sheƙe wasu ‘yan bindigar da dama.

Kazalika, ya ce sojojin sun sake samun nasarar lalatawa tare da kama wasu makamai da motocin yaƙi na mayaƙan a wurare da suka haɗa da yankin ƙaramar hukumar Gombi a jihar Adamawa, da ƙauyukan Rann/Rumirgo da Biu da Bama da Mafa da kuma a yankin ƙaramar hukumar Dikwa, jihar Borno da sauransu.

Bugu da ƙari, ya ce sojoji sun ƙwato dabbobi da aka sace guda 101 tare da ceto jami’an ‘yan sanda su 20 da aka yi garkuwa da su yayin harin da ‘yan bindigar suka kai a ofishin ‘yan sandan a Buni Yadi.