Yadda haƙowa da cinikin zinare ke ƙarfafa ta’addanci a Arewa maso Yamma

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

An ƙiyasta cewa, Nijeriya tana yin asarar sama da Dala biliyan tara duk shekara saboda haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba — inda kaso mafi yawa ya ta’allaƙa ne da haƙar zinariya.

Wani bincike da jaridar Daily Trust ta gudanar ya gano cewa babbar kashi daga cikin zinariyar da ake haƙowa a Arewa maso Yamma tana komawa hannun masu ta’addanci don su riƙa samun kuɗaɗen sayen makamai ne.

A ƙarƙashin ƙasar Zamfara mai arzikin zinariya, wani ɗan bindiga mai suna Kachalla Mati, wanda ya gaji gawurtaccen shugaban ’yan ta’adda Halilu Sububu, ana zargin yana tara fiye da naira miliyan 300 a mako daga wuraren haƙar zinariya da ba su da lasisi. Ana fitar da wannan zinariya ta ɓoye zuwa ƙasashen waje, inda ake sayar da ita don samun kuɗin sayen makamai, ko kuma ana musanya ta kai tsaye da bindigogi — abin da ke ƙara dagula tsaro a arewacin ƙasar.

Shekaru 35 da suka gabata, wani mai haƙar ma’adanai mai suna Hussaini Isah yana haƙo zinariya a yankin Dan-kamfani na arewa maso yamma ba tare da tsoro ba. Amma yau, yana haƙo ta a ƙasan ƙasa cikin fargaba, yana rayuwa a cikin tashin hankali a sassan jihar Zamfara.

A wancan lokaci, su kan zauna a dazuzzuka suna aiki daga safe har zuwa asuba, suna dogara da haƙar zinariya wajen rayuwarsu.

“Aikin yana da wuya, amma shi ne abin da muke ci da shi kullum,” inji shi.

Yanzu kuwa wannan rayuwa ta rushe, yayin da ’yan ta’adda ke addabar ƙauyukan da ke da arzikin zinariya a Arewa maso Yamma da Arewa ta Tsakiya. Suna kashe mazauna yankuna, suna korar masu haƙar ma’adinai kamar Isah su yi musu aiki da ƙarfi, kamar bayi.

Tsawon shekaru, yankin Arewa maso Yamma na Nijeriya ya kasance cikin barazanar tsaro da ke fitowa daga ’yan fashi da makami, waɗanda ke cin moriyar gazawar gwamnati da iyakoki marasa tsaro. A da, rikicin noma da kiwo ne ya fara haifar da wannan matsala, amma daga baya suka koma manyan ƙungiyoyin laifuka, suna samun kuɗaɗe ta hanyar satar shanu, garkuwa da mutane, fashi, da kuma karɓar haraji daga al’umma.

Sai dai tun daga shekarar 2022, ɓangaren haƙar zinariya da hannu (artisanal mining) ya zama sabon tushen samun kuɗi ga ’yan ta’adda, wanda ke ƙara tayar da rikici da neman makamai.

Duk da cewa Gwamnatin Tarayya ta tura sojoji don katse musu damar gudanar da ayyuka, ’yan ta’adda kan sake haɗuwa bayan hare-hare, su ƙone ƙauyuka, su raba dubban mutane da muhallansu, su ƙi bin doka. Rahoton haɗin gwiwa na Global Initiatiɓe Against Transnational Organised Crime (GI-TOC) da ACLED ya nuna cewa daga 2018 zuwa 2023, yawan mutanen da ’yan ta’adda suka kashe a Zamfara da Kaduna ya haura 4,758, wanda ya fi yawan mutuwar da masu tsattsauran ra’ayi suka jawo a Arewa maso Gabas.

Zinariya, wacce ke da sauƙin ɓoyewa kuma ba ta da sahun bin diddigi, ta bai wa ’yan ta’adda ikon mallaka da iko. Yayin da tattalin arziki da siyasa ke girgiza a duniya, buƙatar zinariya ta ƙaru zuwa tan 4,606.2 a 2024, bisa bayanan kasuwar duniya. A Nijeriya, inda tsarin kula da ma’adinai ya raunana, wannan ya buɗe hanyar da ta sa ’yan ta’adda suka zama manyan ’yan kasuwa a fannin.

A bisa tsarin kundin tsarin mulkin ƙasa, Gwamnatin Tarayya ce kaɗai ke da ikon kula da harkokin ma’adinai, duk da cewa fannin bai kai kashi 1 cikin 100 na jimillar kuɗin da ƙasar ke samarwa ba (GDP). Sai dai, kuɗaɗen shiga daga wannan fanni sun ƙaru da kashi 16 cikin 100 daga biliyan N345.40 biliyan (dala miliyan 226) a 2022 zuwa biliyan N401.87 (dala miliyan 263) a 2023 – mafi girma cikin shekara goma da suka gabata, a cewar rahoton Nigeria Eɗtractiɓe Industries Transparency Initiatiɓe (NEITI).

Duk da haka, masana sun yi gargaɗin cewa wannan adadi ba ya nuna gaskiyar yawan arzikin da ke cikin ƙasar, domin har yanzu haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba na ci gaba da hana gwamnati samun cikakken riba.

A wani yunƙuri na gwamnati don gyara wannan matsala da kuma samun cikakken bayanin yadda zinariya ke fita daga ƙasar, Ministan Bunƙasa Ma’adinai na ƙasa, Dr. Dele Alake, ya bayyana a watan Yuli cewa ƙungiyoyi sama da 3,000 na ma’adinai ‘yan hannu (artisanal cooperatiɓes) an riga an yi musu rijista.

Baya ga wannan, an ƙaddamar da Shirin Fadar Shugaban ƙasa na Haƙar Zinariya (Presidential Artisanal Gold Mining Initiatiɓe — PAGMI) a 2019, wanda ke da manufar sayen zinariya daga masu haƙar ma’adinai da hannu ta hanyar National Gold Purchase Programme, domin tabbatar da cewa kuɗaɗen shiga suna shiga asusun gwamnati kai tsaye.

Sai dai a cewar masu haƙar ma’adinai kamar Hussaini Isah da sauran jama’a a yankunan Anka da Maru na Zamfara, da kuma Birnin Gwari a Kaduna, wannan shirin bai kai garesu ba. Domin ’yan ta’adda sun mamaye wuraren haƙar zinariya, suna da ikon mallakar wuraren, abin da ya sa gwamnati ta kasa shiga cikinsu.

A ƙarshe, hakan ya sa wadatattun ma’adinai a yankunan suka koma hannun masu ƙungiyoyin da ba na gwamnati ba, wato ’yan bindiga.

A cikin wannan binciken, an gano cewa shugaban ’yan ta’adda Kachalla Mati, wanda ke gajiya da Halilu Sububu, yana haƙowa da fitar da zinariya ta haramtacciyar hanya da kimarta ta kai naira miliyan 300 (dala 196,000) a mako. Babbar kashi daga cikin wannan zinariya ana musanyanta da makamai ko kuma ana sayar da ita a kasuwannin ba bisa ƙa’ida ba a yankin Sahel.

Daga nan kuma, zinariyar tana isa birnin Dubai a ƙasar Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa (UAE), wanda ya zama na biyu mafi girma wajen kasuwancin zinariya a duniya, kuma wurin da ake yawan sayar da zinariyar Nijeriya da aka fitar ta ɓoye.

Waɗannan haramtattun harƙalloli ne ke ƙara bai wa ’yan ta’adda damar samun makamai, da kuma ƙarfafa rikici da rashin tsaro a arewacin ƙasar.

Kafin shekarar 2022, ba a da hujja mai ƙarfi da ta nuna cewa ’yan ta’adda na da hannu kai tsaye a harkar haƙar zinariya, saboda aikin yana buƙatar salon ƙwarewa da ba irin salonsu ba. A wancan lokacin, satar shanu, garkuwa da mutane, da karɓar haraji daga al’umma su ne manyan hanyoyin samun kuɗi ga ’yan bindiga.

Domin fahimtar yadda wannan ke gudana, manema labarai sun ziyarci garin Birnin Gwari a Jihar Kaduna — yankin da tsohon gwamnan jihar, Nasir El-Rufa’i, ya taɓa cewa “yana da zinariya fiye da ta ƙasar Afirka ta Kudu.” Amma yanzu shi ne cibiyar ayyukan ’yan bindiga a jihar.

Hanyar Kaduna zuwa Birnin Gwari mai nisan kilomita 126 ta kasance cikin haɗari, saboda da yawa sun sha kamuwa da hare-haren ’yan bindiga a can. Amma bayan yarjejeniyar zaman lafiya da aka cimma a farkon shekarar 2025 tsakanin gwamnati da ’yan bindiga, hanya ta fara samun ɗan natsuwa. Duk da haka, masu tafiya har yanzu na cikin fargaba, saboda irin waɗannan yarjejeniyoyi ba sa dawwama.

A tsawon tafiyar, ana iya ganin ƙauyuka da aka ruguza kamar Unguwar Yako, Tsohuwar Udawa, da Manini — wurare da suka zama kufai saboda hare-haren ’yan bindiga da garkuwa da mutane. Mutane da dama sun tsere daga gidajensu, gonaki sun lalace, ƙauyuka sun zama shiru.

Masu kasuwanci suna tara zinariya, sannan su kai ta kasuwar Pollo da ke Gusau, inda ake sayarwa zuwa manyan ’yan kasuwa daga Abuja ko kuma Dubai.

Aliyu Adamu Almajiri, mai magana da yawun ƙungiyar masu saye da sayar da zinariya ta Zamfara, ya tabbatar cewa zinariya daga wannan kasuwa tana kaiwa Dubai, kuma ana yin cinikin kimanin naira miliyan 250 ($164,000) a kowane mako — ƙasa sosai idan aka kwatanta da lokacin da ba a da matsalar tsaro.

Amma ba masu sayar da zinariya kaɗai ke sha’awar Dubai ba. Zinariyar da ’yan bindiga ke haƙowa ma tana bi ta ɓoyayyun hanyoyi zuwa kasuwannin ba bisa ƙa’ida ba, inda take zama tushen kuɗin da ke goyon bayan ta’addanci a yankin.

By ukarofi